Yan Ci-ranin Musulunci Da Sahabban Annabi (ﷺ)



Ramadaniyyat 1442 [16]

'Yan Ci-ranin Musulunci Da Sahabban Annabi (ﷺ)

1. Shi ya sa za a ga hatta kafirai 'yan ci ranin Musulunci (orientalists), babban abin da suka saka a gaba shi ne zargin sahabban Annabi (ﷺ) da tuhuma iri-iri, saboda sun san cewa, su ne jagororin shari’a. Babu wata shari’a da ta samu gatan da shari’ar Musulunci ta samu. Hakanan babu wani Annabi da ya samu gatan da Annabi (ﷺ) ya samu. saboda almajiransa sun kasance nagartattu masu amana, masu gaskiya, kuma masu kula da dukkan abin da ya yi, domin su karantar da al’umma.
2. Hakan ta sa wadancan 'yan ci rani suka fi bayar da karfi a janibin sahabban Annabi (ﷺ), domin su zarge su da yi wa Annabi (ﷺ) karya da ruwaito abubuwan da bai fada ba, su jingina masa. Saboda sun san idan suka soki daya ko biyu ko uku daga cikinsu, to sauran ma sun saka shakku a kansu. 
3. Saboda haka sai suka dubi manyan sahabbai wadanda suka fi kowa yada hadisan Annabi (ﷺ) domin damar da suka samu ta tsawon rai da kuma rashin haduwa da wasu abubuwa da za su dabaibaye su. Suka isar da wannan sako na Annabi (ﷺ). Sai suka rika sukar su. 
4. Daga cikin sahabban da suka fi yi wa dirar mikiya akwai Sahabi Abu Huraira (R.A), sabdoda zamantowarsa wanda ya fi kowa ruwaito hadisai masu yawa daga Annabi (ﷺ), domin sun san idan har suka sun rushe shi, to sun rushe hadisai da dama daga cikin hadisan Annabi (ﷺ).
5. Hakanan suka yi wa Anas dan Malik (R.A) kasancewarsa shi ma ya rawaito hadisai masu yawa daga Annabi (ﷺ) kuma Allah ya yi masa tsawon rai, ya dade yana yada iliminsa, kamar yadda kuma ya samu almajirai masu dimbin yawa, har ya hada iyaye da ‘ya’yansu da jikokinsu duk suka yi ruwaya daga wajensu. Shi ma suka fahimci idan sun yi nasarar rushe shi, to babu shakka sun yi wa addinin Musulunci barna ba 'yar kadan ba.
6. Daga cikin manya-manyan 'yan ci ranin Musulunci na kasahen yamma wadanda suka jagoranci yakin bata sahabban Manzon Allah da cin zarafinsu da tuhumar su da karya akwai: (1) Ignaz Goldziher (1850-1921) mutumin kasar Hungry. Shi ne Bayahuden da ya nuna tsana da kiyayya ga koyarwar Musulunci da Sunnar Annabi (ﷺ). Ya yi rubuce-rubuce da da yawa da suka danganci shari'ar Musulunci da hadisan Annabi (ﷺ). Ya jagoranci makiya Musulunci wajen jefa shakku da tantama a kan sahabban Annabi (ﷺ) da hadisansa. 'Yan ciranin Musulunci da 'yan koransu sun dauke shi a matsayin baban shehi masanin addinin Musulunci da suka dogara da rubuce-rubucensa wajen tayar da kura a kan hadisan Annabi (ﷺ) da sahabbansa. Daga cikin littattafansa akwai: (Muslim Studies, Albany 1977), (Introduction to Islamic Theology and Law. Princeton University Press, 1981 ). Daga cikin manyan almajiransa akwai:
 2) Joseph Schacht (1902-1969) dan asalin kasar jamus Biritaniya. Ya zarme sosai wajen tumar sahabban Annabi (ﷺ) tabi'ai da malaman fikihu a kan cewa, su ne suke zauna suka tsara wadannan hadisan, suka jingina su ga Annabi (ﷺ) da sunan hadisansa. Daga cikin rubuce-rubucensa akwai littafinsa (Re-evaluation of Islamic Tradition, JRAS, 1940).
7. Wadannan arna da 'yan koransu sun san cewa, duk sadda aka saka shakka a kan daya daga cikin sahababai, to sauran ma duk za a yi shakka a kansu, daga nan duk sai a rushe su. Idan kuma aka rushe su to an rushe Musuluncin an kuma rushe Alkur’anin shi kansa. Saboda sune suka dauko dakon Alkur’ani suka karantar da al’umma. 
8. To wannan dalili shi ne ya sa wannan babban zindiki da muka amabata a baya, yake fada wa Haruna Rashid cewa, suna fara koya wa yaransu kin sahabban Annabi (ﷺ) ne, don sun san su ne masu ruwaito addini, to idan aka rusa masu nakalto shi, to addinin ma ba zai yi wahala a rusa shi ba.

https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)