KODA MUTUM MAKIYINKANE KADA KAYIWATSI DA ABINDA YAKE FADI...



KODA MUTUM MAKIYINKANE KADA KAYIWATSI DA ABINDA YAKE FADI...

Yana dakyau Gwamnatin tarayya data jihohi suyi amfani da maganar da Sheik Gumi yake fadi, kuma yake basu shawa akan Fulani musamman fulanin da suke cikin daji...

Sheik Gumi yayi wata magana, alokacin da Dalibai suka kaimashi ziyaran sallah. Acikin bayanin da yake masu yake cewa: 

Yana tsoran kada Fulanin nan yakasance suzama masu azaba agaremu, domin sun yarda ayi sulhu dasu, kamar yadda Allah yace:

(۞ وَإِن جَنَحُوا۟ لِلسَّلۡمِ فَٱجۡنَحۡ لَهَا وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِیعُ ٱلۡعَلِیمُ)
[Surah Al-Anfal 61]
Kuma idan sun karkata zuwa ga zaman lãfiya, to, ka karkata zuwa gare shi, kuma ka dõgara ga Allah: Lalle ne Shĩ, Mai ji ne Masani.

Amma ita Hukumar taki yarda da ayi Sulhu dasu. 
 
To kinyar da datayi Allah zai iyasanya Fulanin su azabtamu, kamar yadda Allah yasanya turawa suka azabtar damu alokacin da suka nememu damu yanta bayi mukaki. 
Kamar yadda Allah yace:

(فَلَا ٱقۡتَحَمَ ٱلۡعَقَبَةَ)
[Surah Al-Balad 11]
To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba?

(وَمَاۤ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡعَقَبَةُ)
[Surah Al-Balad 12]
Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã?

(فَكُّ رَقَبَةٍ)
[Surah Al-Balad 13]
Ita ce fansar wuyan bãwa

Gaskiy yakamata Gwamnati tasake nazari sosai, akan matsayar da tadauka, cewa babu sulhu tsakaninta da Fulanin dasuke daji sai dai aje ajefamasu bama bamai akarkashe su, kawai lokaci daya. 

Wannan matsayar da Hukuma tadauka kuskurene babba, domin suma sunada hakki amatsayinsu na yan kasa masu yanci, sannan Bama baman da ake jefamasu, be shafan su masu ta'addancin, sai dai wadanda basuji basu gani ba. Wannan yanuna Hukuma tana kashe mutane wanda basu da alhakin akashesu...

Abinda yakamata Gwamnati tayi sai ta dauki shawaran da Sheik Gumi yabata, domin ya shiga dajin tare da wakilan Gwamnati, kuma agaban su wadannan wakilan Gwamnatin sunji Fulanin sunyarda, sunaso azo azauna dasu, ayimasu afuwa, kuma suma abasu duk wasu hakkokinsu, amatsayinsu na yan kasa masu yanci. A gina masu makarantu, masu ilimi acikinsu asakasu a ma'aikatunda suka dace, awaremasu inda shanayensu zasuyi kiwu, da kuma inda zasuyi noma, sannan kuma agina masu asibitocinsu dana dabbobinsu. Nonon da ake tatsowa daga shanaye, shima Gwamnati tagina wurare yadda za a rika ingantashi, Gwamnati tasamar masu da aikinyi, sannan kuma ga kudi yana shiga asusun Gwamnati. 

Wannan itace hanyar da yakamata Hukuma tabi, dan asami zaman lafiya, domin mutane suke shan wahala idan ankama wani nasu...

 Agabana naji ana ciniki da aka dauki wasu daliban Makaranta a nan jihar kaduna, abinda suke cewa wakilin iyayen daliban Makarantar. Idan basu hada kudin da suka gayamasu ba, zasu kashesu kuma ba suda hasara Gwamnati ce zatayi hasara, domin dalibai ne idan sungama karatu, daga wanda zai shiga soja sai maiyin police sai ma'aikcin asibiti,

 HUKUMA kunji, yarage gareku. Abin sani shine: akwai Hisabi ranar kiyama akan nauyin dake kanku, duk wata rai da aka kashe ko aka wahalarda ita nauyin yana kanku.

Muna Addu'ah Allah yabude zucciyar Gwamnati tagane abinda Dr. Gumi yake fadimata Gaskiya ne ba kiyayya yakeyi da ita ba, Allah yabamu zaman lafiya a Jiharmu kaduna da kuma kasa baki daya. Amin 

🖊
Dan uwanku a Musulunci 
          Abdallah Umar 

Date: 31 July 2021
Post a Comment (0)