YAYA MUTUM ZE ZAUNA DA ƊAN UWANSA ƊAN SHI'AH?



YAYA MUTUM ZE ZAUNA DA ƊAN UWANSA ƊAN SHI'AH?
.
.
*Tambaya ta 7,333:*
=
Idan mutum yanada ɗan uwa ɗan shi'a, uwa ɗaya uba ɗaya yaya zaiyi dashi wajan mu'amala???
=
=
Amsa
=
_Toh yadda zeyi shine duk wani haƙƙi na ƴan uwantaka seya sauke masa, sannan duk tarayyarda zasuyi toh yadinga duba maslaha dakuma ɓarna, idan kana ganin cewa inka ƙaurace masa kadena hulɗa dashi hakan ze iya sawa yabar shi'ancin toh seka ƙaurace masa. Amma idan kana ganin cewa koda ka ƙaurace masa baze bari ba toh shikenan kada ka ƙaurace masa amma duk wani abunda kaga yana aikatawa na shi'anci kada ka ƙarfafeshi akai, ka fito fili ka nuna masa baka tare dashi akan wannan aikin, sannan kuma kadinga masa nasiha akan hatsarin shi'a da sharrinta domin yawancin mutanenda suke shiga shi'a jahilcine yake kaisu amma basu santaba, kamar yadda Ibnu Taimiyyah yake cewa babu mutanenda suke karɓan addinin shi'a daga ƙauyawa sekuma jahilai. Toh seka dinga tura masa wa'azozin malamai waɗanda sukayi akan hatsarin shi'a sanna kuma karka goyi bayansa akan duk wani abunda yazo dashi na shi'anci. Amma duk wata mu'amala ta zumunci wannan ku cigaba dayi sedai karka yarda wani abu na addini yana hadaka dashi musamman idan kai bame karatu bane, amma idan kanada ilimi akan usul da mabàdi'u na ahalis sunnah kuma kasan usul da mabàdi'u na shi'ah toh wannan kana iya biye masa kuna maganar addini domin insha Allahu baze maka tasiriba sedai kai kayi masa. Sannan kuma kayi ƙoƙari kadunga nuna masa mu'amala me kyau karka ha'inceshi karka cutar dashi amma kafito ƙarara kanuna baka tare dashi akan mummunar aƙidarsa****_
=
=
Allah Yasa mudace
 .
.
*DAGA ZAUREN*
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس تعليم الكتاب والسنة* 
📓📔 
Watsaps
08036222795
09031200070
.
°
Yau
25-12-1442
04-08-2021
=
=
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
Domin samun shafinmu a Telegram 
https://t.me/joinchat/IqYRYUcyJstfI3sSYKPKsQ
°
Kuna iya samun tsoffin darussanmu kai tsaye ta cikin wannan shafin
http://zaurenkitabuwassunnah0.blogspot.com
*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ اللهم ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ*
.
*Subhanakallahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illa anta astagfirukallahumma wa atubu ilaika*
Post a Comment (0)