MAI YASA KHALID BN WALID BAI MUTU A FILIN YAQI BA?

*HIKIMAR UBANGIJI*🌹🌹🌹🌹


MAI YASA KHALID BN WALID BAI MUTU A FILIN YAQI BA


   wannan wata fa'ida ce mai girman gaske da take saka nutsuwa cikin zuciyar duk wani mumini  

  *SHEIKH ABDULFATAH ABU GUDDA* Yana bada labari yake cewa "Nayi tafiya zuwa kasar *Indiya* sai muka hadu da babban malamin indiyan nan masani hadisi da fiqhu, wato *MUHAMMAD BN YA'AQUB ANNANUTAWI* sai yake ce min shin kasan hikimar da yasa Khalid bn walid ya mutu akan shimfidarsa bai mutun a filin yaqi ba, tare da san da yake ya mutu a filin yaqi, tare da kasancewarsa a bagen yaqi sama da 120 yana dauke da tutar yaqi wanda babu wani waje ajikinsa ba tare da ka samu wani tabo na suka ko yanka da mashi ba? 
    Sai SHEIKH ABDULFATAH ABU GUDDA yace a a ban sani ba, 
     Sai SHEIKH YA'AQUB yace malamai sun gaya mana cewa manzan Allah saw ya yiwa Khalid bn walid da laqabi da ZARARREN TAKOFIN UBANGIJI, idan aka kashe shi a filin yaqi kamar an karya takofin ubangiji ne, shi kuma takofin ubangiji har abada ba'a karya sa, saboda kada mutane su zo suna cewa an kashe takofin ubangiji an karyata, sai ubangiji ya zaba masa ya mutu akan shimfidarsa, sai Sheikh Abdulfatah Abu gudda yace : na rantse da Allah wannan fa'idar da na samu, da ace babu abun da ya kawoni kasar indiya sai akan wannan maganar da tabbas ta fiyata tayi riba.

*Rubutawa...✍️✍️✍️✍️✍️*
        *Dalibi mai neman ilimi*
        *Nazifi Yakubu Abubakar*
         *(Abu Rumaisa)*
       🥏08145437040🥏
Post a Comment (0)