Mazaje a samu ayi aure idan da hali...



Mazaje a samu ayi aure idan da hali... 

Na fahimci wani hanunka-mai-sanda da akeyiwa tuzurai duk son suyi zucia suyi aure, abubuwan matakai ne, ku saurara ku ji su: 

Matakin farko: ana samaka abinci a cooler (food flask) akai ma dakinka, duk lokacin da ka dawo kaci abicinka.
A wannan mataki shekarunka basuda yawa

Mataki na biyu: asa maka a cooler, amma se kadawo kana tsammanin ankai ma daki, se kaga babu, se kayi magana ace kaje yanacan kitchen ka dauka... 😀 Shekaru sun fara tafiya kenan

Mataki na 3: yara su fasa cooler din ko ta qone.. 

Mataki na 4: se a canza maka daga cooler akoma zuba maka abinci a cikin kwanon silver ko kwatano... 

Mataki na 5: yara su batar da murfin kwanon akoma rufe kwanon silver da murfin Langa ko roba..

Mataki na 6: ka dawo se kaje daukan kwanon abincin ka kaga wayam, ka tambaya ace, "yi haquri, munyi Baqi ne yau a gidan muka dau naka muka basu" 😀😀
Mataki na 7: a daura maka kwanon abincin akan window dakinka..
A wannan mataki idan baka Lura bah kadawo garin gaggawan bude window dakin ka seka barar da abincin ka 😃
Mataki na 8: kadawo cin abinci ace ai anyi rabiya an manta da Kai .. 😁😁😁

Haba Malaam! Wai har yanzu ace baka gane saqon da ake isarma bah??? 

Akwae wasu matakai da yawa bayan wadannan 🤣🤣🤣🤣

Ka daure kayi aure idan akwae hali tuzuru, in ba haka bah nan gaba a murfin tukunya za'a nah zuba mah abinci... 😀😀😀

Nayi nan kafun wani ya kamoni 
🏃🏃🏃

Allah yasakawa iyayen mu da suke haqurin ciyarda mu na fisabilillah..

Allah ya bamu ikon yin aure😊😊😊

Malam a wani mataki kake???
Post a Comment (0)