WATANNI MASU ALFARMA



WATANNI MASU ALFARMA

Watannni masu alfarma guda huɗu su ne, *RAJAB, ZHUL QA'ADA, ZHUL HIJJA, MUHARRAM* 
         Shaikh Ibnu Uthaimeen Allah ya masa rahama yana cewa, "lalle a yau zaku fuskanci watanni masu alfarma guda uku jerarru (zhul qa'ada, zhul hijja, muharram), kada ku zalunci kawunanku acikinsu, ku lizimci dokokin Allah, ku tsayarda farillan da Allah ya dora muku, ku nisanci abunda ya haramta muku, ku sauke hakkokin dake tsakaninku da Ubangijinku , da wanda ke tsakaninku da sauran bayin Allah". 

الضياء اللامع ٩/٧٠٤ 

Imamul Qatada Allah ya masa rahama yana cewa "kada ku zalunci kawunanku acikin wadannan watanni, saboda lalle sabawa Allah acikinsu ya fi kowane girman laifi da zunubi akan wasu watanni da ba suba, duk da cewa shi sabo a kowane lokaci yana da girma, sai dai Allah yana girmama abunda yaga dama daga cikin al'amura".

تفسير ابن جرير

Imamul Qurdubi Allah ya masa rahama yake cewa, "Allah ya kebance watanni guda hudu masu alfarma ne da ambato da kuma hani da yin zalunci acikinsu saboda girman sha'aninsu, duk da cewa zalunci haramunne akowane lokaci..."

تفسير القرطبي ٨/١٣٥

# Zaurenfisabilillah

Telegram:

Telegram:https://t.me/Fisabilillaaah

Facebook:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Post a Comment (0)