Sahabban Annabi (ﷺ) A Gidan Banu Hashim Da Gidan Banu Umayya



Ramadaniyyat 1442H [25]

Dr.Muhd Sani Umar (Hafizahullah)

Sahabban Annabi (ﷺ) A Gidan Banu Hashim Da Gidan Banu Umayya
_______________________________

1. Abin da wasu marubuta da dama suke kokarin su nuna na samuwar rashin jitiwa tsakanin gidan Banu Hashim da gidan Banu Umayya, wannan duka molan-ka ne, ba gaskiya ba ne.
2. Yadda gaskiyar lamarin yake kuwa shi ne, Musulunci da ya zo ya lullube duka wadannan gidaje biyu. Kamar yadda aka samu wasu daga cikin Banu Hashim sun shiga Musulunci tun daga farko, to hakanan ma aka samu wasu jama'a daga cikin Bunu Umayya wadanda suka shiga Musulunci tun da farko, kamar irin su Amru dan Sa'id dan Asi, da dan'uwansa Khalid dan Sa'id, da kuma Usmanu dan Affan da Abu Huzaifa dan Utba.
3. Hakanan kamar yadda wasu daga cikin Banu Umayya ba su karbi Musulunci ba sai daga karshe, to haka su ma a cikin Banu Hashim akwai wadanda sai daga karshe ne suka Musulunta.
4. Hakanan kamar yadda wasu daga cikin Banu Umayya suka nuna kiyayyarsu ga Annabi (ﷺ), haka su ma a cikin Banu Hashim an samu wadanda suka fito fili suka nuna kiyayyarsu gare shi, kamar Abu Lahab dan Abdulmuddalib da Abu Sufyan dan Haris dan Muddalib.
5. Ayoyin sun sauka da kakkausan suka ga Abu Lahab, amma babu wata aya daya takamaimai da ta sauka don sukan wani dan Banu Umayya.
6. Annnabi (ﷺ) ya yi aure daga gidan Banu Umayya, wato ita ce Ummu Habiba 'yar Abu Sufyana, amma bai auri wata mata daga gidan Banu Hashim ba. Kuma ya aura wa dan gidan Bunu Hashim 'yarsa daya, wato Aliyyu dan Abu Dalib (RA), amma kuma ya aurar da 'ya'yansa mata uku ga gidan Banu Umayya.
7. Don haka Musulunci bai tare a gida daya ba ballanta a ce daya gidan yana nuna gabarsa saboda haka. Musulunci ya hada zukatansu sun zama 'yan'uwan juna da ni'imarsa. Su duka Musulunci ya sanya musu riga guda. Gaba dayansu suna son Musulunci, suna girmama shi, suna kuma alfahari da shi, kuma kowane daya daga cikinsu yana son ya samu rabonsa mai tsoka daga gare shi.

https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)