Sahabban Annabi (ﷺ) Kakaf Ba Munafuki (3)



Ramadaniyyat 1442H [23]

Dr muhd Sani Umar (Hafizahullah)

Sahabban Annabi (ﷺ) Kakaf Ba Munafuki (3)
_____________________________

1. Su kuwa mutanen kauyuka, al'amarinsu ya fito sarari bayan wafatin Manzon Allah (ﷺ), munafukan da ke cikinsu, nan da nan suka yi ridda. Kuma daman ba su yi wani zama tare Manzon Allah (ﷺ) ba wanda har za su cancanci sunan sahabbai a shari'ance. Wanda kuwa daga baya ya musulunta, to wannan sunansa tabi'i.
2. Su kuma wadanda suka musulunta bayan bude Makka, to sau tari akan yi kuskure game da lamarinsu, har ma ka ji wasu suna cewa, ta yaya da rana tsaka kawai a ce sun rukida sun zama Muslmin kwarai, tare da cewa sani kowa ne, ba su musulunta ba sai da suka ga uwar-bari, suka ga in sun ci gaba da zama a kan shirka, to za su cutar da rayuwarsu ne kawai. 
Amma magana ta gaskiya ita ce, shi Musulunci tun farkonsa abu ne mai tasirin gaske a zutakatan jama'a. Abin da zai tabbatar maka da haka abubuwa uku ne:
Na daya, abin da Allah ya labarta mana na fadar kafirai cewa: “Kada ku saurari wannan Alkur’ani, ku rika yin hayaniya a cikinsa don ku yi rinjaye.” [Fussilat, aya ta 26].
Da kuma fadarsu cewa: “Lalle saura kiris ya vatar da mu daga ababen bautarmu, ba don mun yi hakuri a kansu ba.” [Al-Furkan, aya ta 42].
Na biyu, irin yadda kafirai suka yi ta kokarin hana mutane sauraren Alkur'ani, har sai da abu ya kai ga cewa, idan yau bako ya shigo garin Makka sai sun gargade shi da cewa, kada ya kuskura ya saurari wata magana daga Annabi (ﷺ). Ga kuma yadda suka yi wa mutumin da ya ba wa Abubukar (RA) mafaka sharadin cewa, kada ya bar shi ya rika karanta Alkur'ani inda mutane za su ji shi. [Bukhari#2297].
Na uku, wanda shi ne ya fi fitowa sarari, watau yadda tun farko 'ya'yan manyan kafiran Makka suka rika musulunta suna guduwa suna kaurace wa iyayensu, daga cikinsu akwai Amaru da Khalid 'ya'yan Abu Uhaiha Sa'id dan Al'As, da Walidu dan Walidu dan Mugira, da Abu Huzaifa dan Utba dan Rabi'a da Hisham dan Asi dan Wa'il da Abdullahi da Abu Jandal 'ya'yan Suhailu dan Amru, da sauransu. Wadannan duka iyayensu su ne manyan-manyan Kuraishawa, kuma masu fada a ji, masu wadatar dukiya a cikinsu. Amma duk da haka 'ya'yansu suka guje musu suka karvi Musulunci.
3. Ka lura da wannan sosai. Sau tari marubuta idan suka tashi ambaton wadanda suka fara shiga Musulunci sukan ce, 'wasu ne raunana', har mai karatu ya rika zaton sun musulunta ne saboda rauninsu da kuma yadda suke jin haushin masu karfi, da suna son su dau fansa a kansu, domin wai su wadannan raunanan ba su da wani shugabanci ko wata wadata da za ta hana su karvar gaskiya da jure wahala.
4. Amma alalhakika abin ya fi karfin haka. Kawai dai manya-manyan sun nuna taurin kai ne da girman kai, mutanensu kuma suka ji tsoro suka bi su, tare da irin tasiri da Musulunci ya yi a cikin zukatansu. To amma akwai daga cikin matasansu masu karfin hali da suka musulunta suka sadaukar da matsayinsu da shugabancinsu da wadatarsu, suka yarda da duk wata wahala da za su fuskanta a rayuwarsu ta gaba.
5. Musulunci kuma ya ci gaba da tasiri a cikin zukatan sauran jama'a. Musulunci ya ci gaba da yaduwa a cikinsu har bayan hijirar Annabi (ﷺ) zuwa Madina.
6. Sannan kuma bayan an yi sulhun Hudaibiyya tsakanin Musulmi da Mushirikan Makka, Musulmi suka samu damar gauraya da wadanda ba Musulmi ba, kowa kuma ya sami damar yi wa dan'uwansu na kusa da'awa ko wani abokin huldarsa. Wannan ya ba wa Musulunci damar yaduwa cikin gaggawa. To a wannan lokaci ne wasu manyan shugabanni na kuraishawa suka Musulunta, irin su Khalid dan Walid da Amru dan Asi da Usman dan Dalha da sauransu. Musulunci ya ci gaba da tasiri a cikin ragowar jama'ar Mushirikai.

https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)