💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁
MUJALLAR FINA-FINAN INDIYA
💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁💎🍁
KE GABATAR MUKU DA SHIRIN
༄🌼༄🌼❄️✿🌀...♡...🌼༄🌼༄
MATA A FINA-FINAN INDIYA
༄🌼༄🌼❄️✿🌀...♡...🌼༄🌼༄
Kashi na (05)
Tare da
•----------•✬(✪)✬•----------•
Haiman Raees
•----------•✬(✪)✬•----------•
•┈┈••♡🍃♡••┈┈•
23rd August 2021
•┈┈••♡🍃♡••┈┈•
SHIN KO BOLLYWOOD TA CANJA YADDA AKE GANIN DARAJAR MATA A INDIYA DA MA DUNIYA BAKI ƊAYA?
CI GABA
In muka koma shekarun 50s kuwa, jaruma Madhubala ita ce macen da ta fi kowacce shahara a wannan lokacin. Sai dai saɓanin irin yanayi na 40s, hotonta ko zubin da ake ganinta da shi ya sha banban da na waɗanda suka gabace ta. Sau da dama mutane na ɗaukar jaruma Madhubala a matsayin wata alama ce ta salo da iya kwalliya mai zaman kan shi. In kuwa har jarumar zamanin 50s za ta iya zama wacce ake gani har a kwaikwaya a fannin sa kaya, to tabbas wannan alama ce da ke nuna cewa canji ya durfafo Bollywood.
Domin samun tabbacin wanzuwar wannan canji, ku kalli waƙar 'Aaye Meherbaan' ta cikin shirin Howrah Bridge (1958) ku ga yadda jaruma Madhubala ke cashewa cikin kaya masu nuna surarta, to ba ma wannan ne kaɗai matsalar ba, yanayin jin daɗi da take nunawa a fuskarta shi ya fi jan hankalin 'yan kallo sosai a wancan lokaci. Wannan irin ƙarfi hali da kuma bushewar ido da take da shi, shi ne alama ta fili da mutum zai iya fahimtar cewa lallai yadda mata ke fitowa a cikin fina-finan Indiya ya fara canjawa.
Shekarun 60s da 70s su ma sun fuskanci canji mai girman gaske dangane da shigar da mata ke yi a ciki fina-finan Indiya. Wanda wannan canji ya fara ne daga ƙarshe-ƙarshen shekarun 50s. Masu shirya fina-finai irin su Raj Kapoor da Yash Chopra ba sa wargi wurin nuno jarumar shirin su da shiga mai bayyana tsiraici. Misali; a cikin shirin Raj mai suna Sangam (1964), Vyjayanthimala ta fito a matsayin Radha Mehra/Radha Sundar Khanna. A matsayinta na babbar mace, ta fara bayyana ne a wata fitowa da aka ɗauka a cikin tafki. A wannan fitowa, an nuno Radha swims tana iyo sanye da rigar iyo a ruwa, sai ta yi amfani da ƙafafuwanta waɗanda suke buɗe wajen fallatsawa Sundar Khanna (Raj Kapoor) ruwa ta hanyar tsokana. A yanzu in wani ya kalli wannan wuri zai ga ai ba komai bane, amma a wancan lokacin abun mai girma ne.
A cikin dai wannan shiri har wa yau, ta hau wata waƙa mai suna 'Main Kya Karoon Ram' wacce ke ɗauke da kalamai waɗanda suka yi tsauri a ji mace na faɗar irin su a wancan lokacin. Sannan kuma akwai inda ta ke sa ƙananun kaya da suka matse ta sosai, da kuma masu bayyana jikinta fiye da ƙima tare da zama a cinyar Sundar ɗin. Waɗannan ɗabi'u duka baƙi ne a wancan lokacin.
A cikin wani shirin mai bada umurni Yash Chopra mai suna Waqt (1965), an nuno Meena Mittal (Sadhana Shivdasani) a fili tana canja kaya a wani wurin wanka. IMDB ta ruwaito cewa kaɗan ya rage da hukumar tace fina-finai ta yanke wannan wuri saboda yanayainsa.
Haka kuma a cikin waƙar 'Aasman Se Aaya Farishta' ta cikin shirin An Evening in Paris (1967), nan ma an nuno Deepa Malik (Sharmila Tagore) da rigar iyo mai bayyana surar jiki sosai.
Wani abun dubawa kuma shi ne, duk waɗannan fina-finai da waƙoƙin sun samu karɓuwa sosai kuma sun shahara, wanda hakan ke nuna cewa fitowa jarumai mata a irin wannan shiga ta samu karɓuwa har ta shahara.
Fim ɗin Raj mai suna Bobby (1973), wanda Dimple Kapadia ta fito a matsayin Bobby Braganza a cikinsa na ɗaya daga cikin fina-finan da suka fara rugurguza darajar mata a fina-finan Indiya. A cikin wannan shiri, Dimple ta fito da surar jikinta fiye da ƙima a wurare daban-daban.
A shekarar 2016, yayin da ya halarci shirin Aap Ki Adalat, Rishi Kapoor wanda shi ne jarumin fim ɗin da kan shi ya bayyana irin yadda wannan fim ya canja yadda mutane ke ganin jaruman mata a Bollywood. Ga abinda ya ce:
“A da, jarumai mata a fina-finan Indiya ana kiran su da 'mata' ne. Bayan fitar Bobby, sai aka koma kiransu da 'yan mata.”
Wannan magana da Rishi Kapoor ya yi, ita ke nuna haƙiƙanin yadda duniya a yau take kallon mata a fina-finan Indiya.
Zan ci gaba in sha Allah.
©️✍🏻
Haiman Raees
# haimanraees
Haimanraees@gmail.com
Miyan Bhai Ki Daring