SHIN BAIKO AURE NE ?



SHIN BAIKO AURE NE ?
*TAMBAYA*❓
:
_Malam an yi min baiko da wani mutum, to shi ne zai yi tafiya sai ya biyo ta gidanmu wai yana so mu sadu, ya yi ta kawo min kabli-da-ba'adi, akan cewa, ai mun riga mun yi aure, ni dai gaskiya malam na qi yarda saboda ina da shakka akai, shi ne nake neman fatawa ?_
:
*_AMSA_*👇🏻
:
_To 'yar'uwa tabbas akwai malaman da suka yi fatawa a Nigeria cewa : baiko aure ne, saidai zance mafi inganci shi ne baiko ba aure ba ne saboda hujjoji kamar haka:_
_1. Abin da aka sani shi ne kuɗin da ake bayarwa yayin baiko ba'a bada su da nufin sadaki, duk da cewa wasu suna dunqulewa su bayar gaba ɗaya, kin ga kuwa inhaka ne, to ai dukkan ayyukan ba sa ingatuwa sai da niyya, kamar yadda ya zo a hadisni da dukkan malaman hadisi suka rawaito._
_2. Bayan an yi baiko mutum zai iya cewa ya fasa, a dawo masa da kuɗinsa, kin ga wannan yana nuna ba aure ba ne._
_3. Hakan zai iya bude hanyoyin barna, don dukkan wani ashararu zai iya kai kuɗi a yi masa baiko da wacce yake so ya yi lalata da ita, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da yake kaiwa zuwa barna._
_4. Yana daga cikin sharudan auren a wajan wasu malaman samun shaidu, kin ga kuwa wani lokacin wanda zai kai kuɗin da za'a yi baiko, zai iya zama mutum ɗaya, kin ga akwai nakasu kenan._
_5. Abin da muka sani a kasar Hausa, sai bayan an yi baiko, ake sanya ranar daurin aure, kin ga wannann yana nuna cewa, baiko daban, aure daban._

_6. Sannan duk mun yarda cewa baiko ba ya wajabta gado tsakanin wadanda akayiwa, idan daya daga cikinsu ya mutu kin ga wannan yana nuna cewa ba aure ba ne, domin ma'aurata suna gadon junansu_
.•
Allah shine mafi sani.

.DR. JAMILU YUSUF ZAREWA_

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*_

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)