YADDA AKE WANKAN HAILA



YADDA AKE WANKAN HAILA

- Za'a tsefe ko kwance kitso gabadayan sa.

- Za'a samu ruwa mai tsarki mai tsarkakewa, sannan a samu magarya *(danye ko busasshe, gari ko wanin sa)*.

- Sai ayi niyyar wankan *(a zuciya)*, sannan ace BISMILLAAH *(ba lallai sai an bayyana ba, motsa baki yayin fadi ya isar)*.

- Sai a wanke hannu zuwa wuyan hannu sau uku.

- Sannan a yi amfani da magarya wurin wanke gaba *(farji)* tare da wuraren da jini ya taba. *Ba'a son amfani da sabulu, domin yana da illa ga farjin mace*. 

- Sannan sai a wanke hannu da sabulu *(musamman anti-bacteria; kamar dettol, septol d.s)*.
- Sannan ayi alwala cikakkiya.
- Sannan a wanke kai sau uku tare da cudawa kwarai domin ruwa ya shiga ya ji'ka tushen gashin kai sosai.

- Sai a wanke 'bari ko bangaren jiki na dama daga sama har kasa, sannan na hagu shima haka.

-Sai kuma a zuba ruwa a wanke jiki gabadaya har zuwa kafafuwa.

*A karshe bayan kammala wanka sai a samu 'kyalle ko auduga (mai kyau) tare da turaren Almiski (mai kyau) a rinka dangwala ana tsarki da shi (wato a shafa a farji da kuma wuraren da jinin haila ya ta'ba). Idan ba'a samu Almiski ba za'a iya amfani da wani turaren wanda ba shi da illa ga farjin mace, amma Almiskin shine yafi domin kiyaye lafiyar mace da kwayoyin halitta dake gaban ta da kuma gusar da karni ko warin jinin haila da makamantan sa*.

TSOKACI:
*_Za'a iya sallah da wannan wankan ba tareda an sake alwala ba; matukar abunda ke karya alwala bai sami mutum bayan wankar ba_*.

Domin karin bayani da kuma ganin nassoshi da maganganun malamai dangane da haka sai a duba:
1. Al - Mugniy na Ibn Qudaamah.
2. Tahdheebus sunan na Ibnul Qayyim.
3. Bulughul maraam na Ibn Hajar (Tare da Takhriji da Ta'alikin Sameer Ibn Ameen Az - zuhairiy).
4. Sahih Fiqhus sunnah na Abu Malik Kamal.
Bakidayan su a karkashin babukan da suka yi bayani dangane da Haila da Wankan tsarki.
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)