YAYA HUKUNCIN MACEN DA BATADA TSARKI TADAU WAYAR TAYI KARATU ACIKI.



TAMBAYA❓

YAYA HUKUNCIN MACEN DA BATADA TSARKI TADAU WAYAR TAYI KARATU ACIKI.

AMSA👇

Alqur'anin Application Nawaya rubutacce wanda ake karantawa, kona sauti wanda ake saurara baya daukar hukuncin alqur'ani cikakke wanda ke rubuce acikin takardu. ya hallata taɓa shi acikin wayar ko karantashi batare da tsarki ba, saboda rubutun alqur'anin dake cikin waya bakamar rubutunsa bane dake cikin takardu, Kawai wasu na'urorine suke bijirowa sannan saisu gushe, ba haruffa bane tabbatattu, waya kuma tahada Qur'anin dawasu abubuwan.
Amma karantashi acikin takardu sharadine kaitsaye sai idan mutum yanada tsarki, Saboda Abunda yazo acikin hadisi shahararre ( Baya halatta adauki alqur'ani ko shafarsa sai wanda yake da tsarki) Dakuma abunda yazo na maganganun sahabbai dakuma tabi'ai, Akan haka jamhurdin malamai suka tafi akai, Shine wanda yake da hadasi haramunne yataba alqur'ani saboda tilawa kowanin tilawa.
Abisa wannan zai bayyana garemu cewa Alqur'anin dake cikin waya da sauran na'urori wanda ake taskance abubuwa acikinsu baya daukar hukuncin Alqur'anin dake rubuce acikin takardu, domin rubutunsa ya saɓa da wanda yake acikin takardu, bazaka samesu da siffofinsu da'ake karantasuba, saidai asamesu asifar yanada na'urar dake bayarda haruffan yayinda aka nema, saita bayyanar dashi ascreen idan kuma ka tsallaka kan wani abun acikin wayar sai haruffan su kau, Abisa wannan yahalatta daukar wayar koshafarta, yahalatta karantashi, koda mutum baida tsarki.
Alqur'anin dake rubuce acikin takardu Bai hallata shafarsa ko taɓa shiba saiga wanda yakeda tsarki kamar yanda yazo acikin hadisi, Amma waya ba'a kiranta Alqur'ani.
Karanta Alqur'ani acikin waya saukakawane ga mai haila, da kuma wanda daukar alqur'anin gaba daya yake masa wahala, ko yake wajan dazai masa wahala yin alwala, saboda rashin tsarki.
Saboda haka ya halatta macen dabata da tsarki ta karanta alqur'ani na appilication, ba haramun bane danta dauki wayar kotayi karatu dashi lokacin da batada tsarki.

Wallahu A'alamu.

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)