ABUBUWAN LURA GA MAI NEMAN AURE KO MACE KO NAMIJI

ABUBUWAN LURA GA MAI NEMAN AURE KO MACE KO NAMIJI


*Abubuwan da ya kamata namiji ko mace su lura dashi wajan neman abokin zama, ya kamata mu lura sosai wajan neman abokin zama saboda idan mutum bai nemarwa kansa abokin zama nagari ba kamar ya rusa wani bangare ne a rayuwar sa.*

*_1. ADDINI: mutum mai addini akan sameshi duk abinda zai aikata zai tuna da hukunci Allah da mazonsa, domin musulunci yakarantar da mu dukkan abinda zamu aikata a rayuwar mu komai kankantarsa._*

*_2. KYAWAWAN DABI'U: wajibine mu lura da kyawawan dabi'u sosai saboda akan samu mai addini amma ba kyawawan dabi'u sai kaga ba zaman lafiya hakanan akan samu mai kyawawan dabi'u amma babu addini sai kaga ba zaman lafiya addini da kyawawan dabi'u yan'uwan juna ne. Idan babu daya daga cikinsu za kaga ansamu tawaya, saboda haka idan aka samu *wadannan abubuwa guda to hakika za'a samu zaman lafiya mai dorewa.*

*Dalili kuwa shine fadin* *_manzon Allah S A W idan wanda kuka yarda da addinin sa da dabi'un sa yazo muku to kubashi aure ,idan baku bashi ba to zaku haifar da fitina a cikin kasa._*

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)