ADMIN A GADON ASIBITI

ADMIN A GADON ASIBITI






Likita: Ya jikin naki?

Admin: Hmmm...gashi nan dai!Da dan sauki.

Likita: kin fara iya cin abinci ne?

Admin: Har yanzu dai bana iya cin abinci sosai. Sai dai dazu ne ma da safe nasha maltina kwalaba 3 da madara gwangwani 2. Nakuma ci balangu yanka ashirin, da kwai guda 4. Nasha yoghurt rabin lita roba daya! Wayyo!!! Bayan nasha magani kuma naci gurasa bandashe da
dankalin turawa. Dazu kuma da kyar naci sakwara malmala biyu. An sayo min dambu na dari naci. Yanzu na gama cin alkubus da romon kai sannan na dan kurbi fura ludayi 10! Likita ka rubuta min Multivite kona samu in dinga cin abinci sosai! 

Wayyooooooo!!!


Post a Comment (0)