ANNABI DA SAHABBANSA // 001



⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖

   ANNABI DA SAHABBANSA // 001
.
Kalmar (Arab) kalma ce ta Larabci wace take nufin Sahara ko qeqasasshiyar qasa wace ba ta fidda tsiro kuma ba a samun ruwa a cikinta, tun tale-tale ake kiran wannan yanki da wannan suna, har ma aka ci gaba da kiran wadan da suka zauna a wurin da sunan, mutum guda kuma a ce masa Arabiy, wato a jingina shi da qasar wurin.
.
Duk wanda yake kallon Taswirar wannan yanki na Larabawa zai ga cewa ya yi iyaka ne ta yamma, a wannan lokaci, da tekun Maliya, wato wanda ake yi masa laqabi da Red sea a Turance, Bahar Ahmar a Larabce, ko mu yi masa fassarar farfaru da Jan teku, haka ya gangara har farfajiyar qasar Yaman in da ya yi iyaka da tekun Indiya ta Kudu, sai ya yi iyaka ta Arewa da qasar Sham da zirin yankin qasar Iraqi, ta Gabashi kuma ga tekun qasashen Larabawa nan da La'ananniyar qasar Iran take qoqarin mamayewa.
.
Wannan suna wato Arab ya dace matuqa da wurin, domin zai yi matuqar wahala wani dan adam ya yi sha'awar zama a yankin, shi ya sa ba a sami baqin haure daga wurare daban-daban wadan da ci-rani zai kai su wurin ba, to bare kuma 'yan mulkin mallaka su yi kwadayin mamaye wurin, kenan za mu iya cewa 'yan qwarorin mutanen da suka zauna a wurin ba su sami cakudewar zuriya daban-daban ba, Allah ya tsarkake su daga qabilun Yahudawa da Nasara na tsawon qarnoni masu dimbin yawa, su kadai suke rayuwa a wurin.
.
Idan muka lura da tarihi da kyau za mu ga cewa wannan yanki na Larabawa ya yi kan iyaka ne da daular Rum ta Arewa maso Yamma, su kuwa mutane ne masu qarfin tsiya, ga dimbin makamai, da yawa daga cikin mazauna daular gumaka suke bauta ma wa, sai kuma daular Iran wace aka sani da Farisa, ita ma tana da qarfi sosai ta bangaren Gabashi kenan, ita kuma Majusawa ke zaune a cikinta, wato masu bautar wuta, ko a Qur'ani mun ga irin karawar wadannan dauloli manya-manya guda biyu, ta Kudanci kuma ga daular Habasha nan, koda yake ba ta yi suna wajen handama da babakere ba amma mun san da zamanta.
.
In ba don rashin mamora da wannan yanki yake da shi ba da tuni dayan wadannan manyan dauloli ta mamaye yankin da sunan mulkin mallaka, wannan yanayi na qasar wato sahara, mai qarancin ruwa, da rashin dausayin noma ya sa Larabawa sun tsira daga damqar ashararai na tsawon lokaci.
.
Ta bangaren qabila kuwa, Larabawa suna da tarin qabilu, amma dukansu dai Larabawan ne masu magana da harshe daya, qabilar Jurhum Larabawa ne 'yan asalin Yaman, wadan da suka bi ta Makka inda lokacin sarari ne kawai wanda bai daukar tsiro ma bare a kira shi da daji, mun riga mun fadi yanayin wurin, samun daddadan ruwa ya sa suka nemi su zauna da Hajar AS, wato matar Annabi Ibrahim AS da danta Annabi Isma'il AS.
.
Ba shakka Annabi Ibrahim AS bai bar su ya yi tafiyarsa ba, ya riqa zagayowa yana duba su, ba wanda zai iya fadin iyakacin zuwansa, tarihi dai ya iya kiyaye wajen guda hudu, lokacin da Isma'il AS ya girma kuma ya koyi Larabci a wajen Jurhum, har ma ya auri diyarsu, daganan aka yi ta yaduwa, amma an tabbatar da cewa kakansa Ibrahim AS Balarabe ne daga qabilar Aar da suka zauna a yankin Iraqi.
.
Babban abin sha'awa a ciki shi ne, wannan rashin cakuda da qabiloli daban-daban da wadannan Larabawan suka yi, ya taimaka matuqa wajen iya kare harshen daga salwanta, kuma su kansu suna iya lissafa maka kakanninsu har na qarshe, da wannan ne Larabawan suke iya qidaya kakanninsu, don haka ba wani abin mamaki ba ne in an sami nasabar da ta dangana Annabi SAW da Ibrahim AS, da yake za mu riqa ambato sunayen wadannan qabilu a cikin wannan doguwar tafiya da za mu yi in sha Allah, to bai zama dole sai mun lissafo su jumlatan yanzu ba.

✍🏼Baban Manar Alqasim
Post a Comment (0)