ANNABI DA SAHABBANSA /002



⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖

   ANNABI DA SAHABBANSA /002
.
Galibin Dalilin Da Yake Sanya Malaman Tarihi Su Koma Asalin Rayuwar Larabawa In Za Su Yi Magana Kan Yadda Annani Saw Ya Yi Fama Da Jama'arsa Ko 'yan Uwansa, Sukan Yi Haka Ne Don Su Fitar Da Mu'ujizar Da Allah Sw Ya Yi Masa Ne, Su Kuma Nuna Munafurcin Maqwabtansu Don Bata Addinin Ko Qoqarin Dushe Hasken Annabin, A Qarshe Dai Hakan Bai Samuwa.
.
Daular Larabawa Kamar Sauran Daulolin Ne Sai Dai Su Sun Kasu Kashi Biyu, Kashin Farko Suna Da Hular Sarki A Matsayin Tsararriyar Masarauta Ta Masu Cikakken 'yanci, Duk Da Cewa A Zahiri Ba Su Da Wani 'yanci Na Azo A Gani, Su Ma Suna Yi Wa Wasu Ne Biyayya, Kashi Na Biyu Kuwa Na Shugabannin Qabilun Ne.
.
Mafiyawancin Shugabannin Qabilunnan Suna Da 'yancin Kansu, Ba Sa Karbar Wani Umurni Daga Wurin Wadancan Sarakunan, Masu Hulunan Su Ne Sarakunan Yaman, Gassan Da Hira, Ban Da Su Sauran Karkatakab Dinsu Ba Su Da Hulunan Mulki, Masu Hulunan Kuma Akwai:-
.
Saba: A Yaman, Nan Ne Sarauniya Biqis Take, Inda Annabi Suleiman As Ya Sa A Dauko Masa Karagarta Daga Inda Yake, Wato Qasar Sham (Wato Gamammiyar Daular Syria, Jordan, Lebanon Da Palastine) Tafiyar Mai Matuqar Nisa Ce, To Yemen Din Ne Dai Ake Ganin Mabubbugar Qasashen Larabawa, Saba A Yeman Take, Ana Ganin Bayyanarsu Tun Kafin Haihuwar Annabi Isa Ne Da Shekaru Masu Dimbin Yawa.
.
In Mun Koma Baya Can Za Mu Gano Cewa Sun Bayyana Ne Kafin A Fara Ambatonsu Tare Da Mahaifiyar Annabi Isma'il As, Don Ana Qimanta Shekaru Dubu Biyu Ne Da Doriya Tsakanin Annabi Isma'il As Da Annabi Saw, Bai Wuce Shekara 115 Kafin Zuwan Annabi Isa Suka Bar Aiki Da Sunan Makrub Suka Koma Saba, Suka Yi Ta Samun Tashin-tashina A Tsakaninsu, Kasuwancinsu Ya Tabarbare, Har Dai Rumawa Suka Yi Awon Gaba Da Kasuwancinsu Ta Hanyoyin Ruwa, Bayan Da Can Suna Da Qarfi Sosai A Qasashen Masar, Hijaz Da Sham.
.
To Bayan Zuwan Annabi Isa As Da Kimanin Shekaru 300 Har Zuwa Shigar Muslunci Cikin Yaman Aka Yi Ta Samun Hargitsi Da Juyin Mulki, Gami Da Yaqoqin Cikin Gida Wanda Hakan Ya Kai Su Ga Sunkuya Wa Mulkin Mallaka, Rumawa Suka Shiga Adan, Suka Buda Wa Habashawa Qofar Da Suka Mamaye Yaman A Karon Farko Shekar Ta 340 Bayan Haihuwar Annabi Isa As, Ta Yadda Suka Yi Amfani Da Gasar Dake Tsakanin Qabilar Hamdan Da Hamir, Yaman Ba Su Sami 'yanci Ba Sai Shekara Ta 378.
.
A Kwatankwacin Shekara Ta 351 Miladiya Abu Nawas, Wato Jagoran Yahudawa Ya Far Ma Kiristocin Najran, Da Niyyar Maishe Su Kiristoci Da Qarfin Tsiya, Da Suka Qi Ya Sa Aka Haqa Ramuka Aka Kunna Wuta Aka Yi Ta Cilla Su Ciki Da Ransu, Qur'ani Ya Fadi Qissar A Suratul Buruj, Zai Yi Kyau Mu San Cewa Dalilin Kiristanci Da Lura Da Abin Da Ya Faru A Baya Ya Sa Rumawa Suka Mara Wa Habashawa Din Ta Yadda Su Kuma Habashawan Suka Sake Mamaye Yaman Din A Shekara Ta 525 Suka Sanya Aryat Ya Shugabanci Qasar.
.
To Sai Dai Ba A Jima Sosai Ba Abrahata Ya Yi Masa Juyin Mulki Da Yawun Sarkin Habashan, Wannan Yankin Bai Ishe Su Ba, Sai Da Suka So Hadawa Da Makka Gami Da Rusa Qa'aba, Har Dai Allah Sw Ya Gama Da Su, Kamar Yadda Muka Gani A Suratul Fil, Daganan Qarfinsu Ya Raunana, Har Yamanawa Suka Nemi Taimakon Iraniyawa Wato Farisawa Suka Kori Habashawan Suka Sami 'yanci, Amma Sai Jagoran Wato Ma'ad Yakrib Ya Bar Wasu Habashawa Sunai Masa Hidima, Su Kuma Suka Sami Sa'a Wani Lokaci Suka Kashe Shi.
.
To Ganin Haka Sai Farisawa Suka Yi Tsayuwar Daka Wajen Taimakon Masarautar Yaman, Amma Kuma Su Ne Suke Jagoranci A Fakaice, Ba Su Rabu Da Su Ba Har Sai Da Hasken Muslunci Ya Ratsa Qasar, Daganan Suka Tattara Yinasu-yinasu Suka Qara Gaba, Sai Dai Duk Da Haka Har Maganar Da Nake Yi Yanzu Hutsawa A Cikin Yaman Suna Karbar Umurni Ne Daga Qasar Iran Din, A Hubbasar Da Qasar Take Yi Na Maido Da Qarfinta Wanda Muslunci Ya Qwace Ya Kuma Tsattsaga Ta.

✍🏼Baban Manar Alqasim
Post a Comment (0)