ANNABI DA SAHABBANSA // 014



⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖

       ANNABI DA SAHABBANSA // 014
.
_Da Yawa In Ka Yi Maganar Zuwan Annabi Saw Kogon Hira Sai Wani Ya Zaci Ya Tare Ne A Can Har Aka Saukar Masa Da Wahayi, Ko Kuma Yakan Riqa Tafiya Ne A Duk Sa'in Da Ya Sami Lokaci, A Zahiri Maganar Ba Haka Take Ba, Ya Riqa Tafiya Ne A Duk Watan Ramadan Ya Tare A Can Har Watan Ya Qare, Sai Dai Da Yake Bayani Ya Bayyana Cewa A Wata Shidan Farkon Annabci Ya Lizimci Kadaituwa, Akwai Yuwuwar Ya Shiga Kogon Kafin Ramadan Din, Sanannan Abu Dai In Abincinsa Ya Qare Yakan Dawo Ya Sake Shiri, Har Ma Ya Taimaka Wa Duk Wanda Ya Kusance Shi Da Dan Abin Da Yake Tare Da Shi, Ba Abin Da Yake Yi A Can Sai Ibada Da Kallon Abin Dake Zagaye Da Shi Na Haluttun Ubangijinsa, Da Wasu Abubuwa Na Rayuwa Da Yadda Ake Gudanar Da Su._
.
_Annabi Saw Bai Taba Samun Natsuwa Da Abin Da Mutane Suke Yi Na Shirka Ba, Sai Dai A Lokacin Bai Da Wata Miqaqqiyar Hanya Mai Tattare Da Shari'a Wace Zai Tafi A Kai Sai Lokacin Da Allah Sw Ya Turo Shi A Matsayin Manzo Da Duk Abin Da Dan Adam Yake Buqata Na Addini Da Rayuwa, Ba Shakka Wannan Kadaita Da Annabi Saw Ya Yi Ta Mantar Da Shi Shagaltuwa Da Duniya, Lamarinsa Gaba Daya Ya Koma Zuwa Ga Mahaliccinsa Ne._
.
_Haka Allah Sw Ya So Annabinsa Ya Yi Tun Shekara Uku Kafin Annabci, Domin Shirin Fuskantar Amana Mai Girman Gaske, Wace A Dalilinta Za A Gyara Wa Duniya Gaba-dayanta Zama, A Kawo Wani Sabon Tarihi A Dora A Ban Qasa, A Taqaice Dai Za A Iya Cewa Annabi Saw Ya Fara Shiga Kogon Hira Ne Da Shekara 3 Kafin Annabci, Duk Dai A Shirye-shiryensa Na Zama Manzo Kuma Jagoran Al'umma Gaba Daya._
.
_Lokacin Da Ya Cika Shekara 40, Wato Mutum Kamili, Daganan Ne Alamun Manzanci Suka Gama Bayyana Masa Gaba Daya, Daga Cikin Abubuwan Da Ya Riqa Gani Akwai Mafarki, Ta Yadda Wahayin Yake Fito Masa Kamar Wulqawar Walqiya, Har Ya Kwashe Wata 6 A Kan Haka, Bayan Nan Ya Shekara 23 Ne A Cikinsa, Kenan Shekarunsa 63 A Duniya, To Bayan Annabi Saw Ya Kwashe Shekara 3 Yana Zuwa Wannan Kogon Lokacin Ne Allah Sw Ya Karrama Mutane Da Samun Manzon Tsira._
.
_Bayan Bincike Mai Zurfi Wanda Malamai Suka Yi Don Tantance Lokacin Da Jibril As Ya Zo Wa Annabi Saw, An Gano Cewa Ranar Litinin Ce Da Daddare 21 Ga Watan Ramadan, Wanda Ya Zo Daidai Da 10 Na Watan Agusta Shekara Ta 610 Miladiya, A Daidai Lokacin Da Annabi Saw Ya Cika Shekara 40 Da Wata 6 Da Kwana 12 A Qidayar Watan Sama Kenan, Wato Daidai Da Shekara 39 Da 3 Da Kwana 12 A Qidayar Watan Bature._
.
_Koda Yake Malamai Sun Yi Ta Samun Sabani Wajen Tantance Lokacin Fara Saukar Wahayin, Wasu Suna Ganin 12 Ne Ga Watan Rabi'ul Auwal Kamar Yadda Ya Zo A Hiqbatun Minttarikh P31, Wasu Suka Ce Rajab, Na Ga Kusan Marubutan Shi'a Duk A Kan Haka Suka Tsaya, Mu Kuma Mun Zabi Ramadan Ne Don A Baqara Allah Sw Yana Cewa: ={Ramadan Watan Da Aka Saukar Da Qur'ani}= A Suratul Qadr Kuma Ya Ce ={Lallai Mun Saukar Da Shi -wato Qur'ani- A Daren Qadr}= Lalatul Qadari Kuwa Mun Fi Ganinsa A Kason Goman Qarshe._
.
_Dalilin Da Ya Sa Muka Zabi 21 Kuwa Ga Watan Shi Ne: Masana Tarihi Kacokan Dinsu Ko Galibinsu Sun Tsaya Ne A Kan Ranar Litinin Aka Fara Saukar Masa Da Wahayi, Wannan Ya Zo Daidai Da Ruwayar Malaman Hadisi Ta Hanyar Qatada, Wanda Aka Tambayi Annabi Saw Azumin Litinin, Sai Ya Ce "A Ranar Aka Haife Ni, A Ranar Aka Saukar Min Da Wahayi" A Wata Ruwayar Ya Ce "Wannan Ranar Ce Aka Haife Ni, A Cikinta Aka Turo Ni A Matsayin Manzo" Muslim 1/368, Ahmad 5/298, Baihaqi 4/286, Hakim 2/ 602._
.
_To Ranar Litinin A Wannan Shekarar Ya Zo Daidai Ne Da 7, 14, 21 Da 28, To Mun Karanta Cewa Ana Samun Lailatul Qadari Ne A Mara Na Goman Qarshen Watan Ramadan, Kenan Koda Yake Tana Zazzaga Mararrakin Da Ke Goman Qarshen Ne, A Wannan Shekarar Dai Ta Fado Ne A 21 Ga Wata, Duba Zuwa Ga Hujjojin Da Suka Gabata Za Mu Gane Cewa Da Daddare Ne, A Watan Azumi, Goman Qarshe, Kuma 21 Ga Wata._
.
_*✍🏼 Baban Manar Alqasim*_
Post a Comment (0)