ANNABI DA SAHABBANSA //025



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //025❤️💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

Najashiy na rufe baki sai Amr bnl As ya yi waje yana ce wa mutuminsa Abdullah bn Rabi'ah "Gobe wallahi zan fito musu ta bayan gida na yi maganinsu" Abdullah ya ce "A'a kar ka yi haka, ai 'yan dangi ne, koda kuwa mun yi hannun riga da su" Amr ya toge a kan ra'ayinsa.
.
Suna haduwa kashe-gare ya ce da Najashiy "Yallabai! Sukan fadi wata babbar magana a kan Isa dan Maryam" sai Najashiy ya sa a kirawo su don ya tabbar, koda suka ji abin da zai tambaye su a kai sai suka tsorata, amma a qarshe suka yanke fadin gaskiya ko a mutu ko a yi rai, suna shiga Najashiy ya tambaye su.
.
Sai Ja'afar bn Abutalib ya ce "Mukan fadi abin da Annabi SAW ya zo mana da shi ne, cewa Isa bawan Allah ne kuma manzonsa, ruhinsa ne ya sanya wa Maryam tana budurwa tsarkakakkiya" da Najashiy ya ji abin da suka ce sai ya ce su tafi abinsu su saki jiki, duk wanda ya yi musu maganar banza za a ci shi tara, daganan ya sanya a mayar musu da kyaututtukansu ya ce rashawa ne ba zai amsa ba.
.
Bayan wannan yunquri na amso masu hijira ya ci tura sai suka gane cewa in fa ba a tsukin inda suke ba ne ba yadda za su yi da wannan abin da ya qi ci ya qi cinyewa, da haka sai wani mugun tunani ya afko musu, wato ko dai su yi wa Manzon Allah SAW takunkumi yadda za su hana da'awar tasa gaba daya ko in haka ta qi yuwuwa su yi masa kisar mummuqe.
.
SUN JA WA ANNABI KUNNE
Da farko dai manyan Quraishawan sun sami Abutalib ne suka ce "Abutalib, kai babba ne kana da shekaru da matsayi a wurimmu, mun yi iya qoqarinmu wajen ganin ka cire hannunka game da dandannan naka amma ka qi, mu kam wallahi haqurimmu ya qare, ba za mu bari a riqa zagin iyayemmu, ana wawanta hankalimmu, ana aibanta allolinmu ba, yanzu kodai ka hana shi, ko kuma mu yi muku kudin goro kai da shi, sauran kuma ya rage ko mu ko ku".
.
Wannan gargadi ya tsaya wa Abutalib a rai, sai ya aika wa Annabi SAW yana cewa "Dana, mutanenka fa sun same ni suna yi min wasu maganganu, ka dube ni ka dubi kanka, kada ka dora min abin da ba zan iya ba" daganan ne Abutalib ya ji a jikinsa cewa gwiwar baffansa ta yi sanyi, sai ya ce "Baba, da za su dora min rana a damata, wata kuma a haguna wai don na bar wannan saqon, ba zan bari ba sai dai na mutu ko Allah ya bayyana lamarinsa"
.
Yana yin shuru sai ya kama kuka, ya tashi ya kama hanya, Abutalib ya kira shi ya ce "Dana je ka fadi abin da kake so, na rantse da Allah ba zan taba bashe ka ba har abada.
.
SUN SAKE DAWOWA WAJEN ABUTALIB
Da dai Quraishawa suka ga cewa Abutalib ya qi daukar wani mataki, kuma Annabi SAW ya ci gaba da abinsa kamar yadda yake so, sai suka dumfari wurinsa da Amara bnl Walid bnl Mugira, wato dan uwan Khalid, suka ce "Ka san dai wannan yaron a tsakanin Quraishawa ya fi kowa dangane da kyau, to ka riqe shi, nauyinsa da komai nasa yana wuyarka, yanzu ya zama danka, mu kuma ka ba mu dancan naka da ya saba wa addininka da na iyayenka, ya raba kan al'ummarsa, ya kuma raina hankalin kowa, sai mu kashe shi, shi kenan an yi raba daidai kenan mun musanya maka"
.
Ya ce "Wannan wace iriyar bankaura ce haka? Ku ba ni danku na wahala da rainonsa, na ba ku nawa ku kashe, wannan kam wallahi ba ta taba sabuwa, sai Mut'im bn Adiy, bn Naufal bn Abdimanaf ya ce " Abutalib gaskiya mutanannan sun yi maka adalci, sun yi iya woqarinsu wajen nisantar abin da zai dame ka, amma kai ba ka son ku daidaita"
.
Ya ce "Wallahi ba su yi min adalci ba, kawai ka yi ninyar ka ci mutuncina ne kai da wadannan da suka yi min taron dangi, don haka je ka yi abin da ka ga dama" wannan kai komo har guda biyu da suka yi zuwa wurin Abutalib a shekara ta shida suka yi bayan annabci, dududu dan qaramin lokaci ne a tsakaninsu.
Zamuci Gaba Inshaa Allaah...

*Gabatarwa: Zauren Sunnah*

*WhatsApp @Zauren Sunnah*
 +2348039103800.
 +2347065569254

*Facebook @Zauren Sunnah*
https://www.facebook.com/groups/552998655501583/

*Follow my Page*
Visit to like my Page-https://www.facebook.
Post a Comment (0)