ANNABI DA SAHABBANSA //026



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //026❤️💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

*YUNQURIN KASHE ANNABI SAW*
Bayan duk wani qoqari na gamsar da Abutalib ya ci tura, sai Quraishawa suka fara tunanin yi wa Annabi SAW kisar gilla, wace ita ce zabi ko mataki na gaba da suke ganin ba wata makawa sai an dauke shi, a maimakon su cimma burinsu a wannan mataki sai ya zamto kuma dalilin musluntar wasu barada na muslunci guda biyu, wato Hamza bn Abdilmuttalib RA da Umar bn Khattab RA, daga cikin cuturwar da Quraishawan suka yi wa Annabi SAW bayan qalubalantar Abutalib:-
.
Wata rana Utaiba bn Abilahab ya zo wajen Annabi SAW ya ce "Na kafurce wa (Wannajmi iza hawa) da wanda aka ce masa (Dana fa tadalla)" sai ya cakumo Annabi SAW ya keta rigarsa, ya yi qoqarin yin kaki ya tofa wa Annabi SAW a fuska, aka yi sa'a bai same shi ba, irin wannan cin zalin da cin mutunci ya sa Annabi SAW ya yi masa addu'ar Allah ya hada shi da wani naman dajin da zai yi gaja-gaja da shi, ilai kuwa, Allah SW ya amshi addu'ar Annabi SAW.
.
Wani lokaci Utaiba ya fita kasuwancinsa da wasu Quraishawa inda suka isa wani qauye dake qasar Sham ana ce masa Zarqa, zai wani gawurtaccen zaki ya fito musu yana zaga su, nan Utaiba ya ce "Wallahi ni zai ci, kamar yadda Muhammad ya yi min wannan addu'ar, kun ga ya kashe ni shi yana Makka ni ina Sham" kamin ka ce haka har zakin ya fada masa ya gama da shi.
.
Daya daga cikin dalilan da suka bayyana qarara cewa wadannan azzaluman kashe Annabi SAW suke son yi shi ne ruwayar Ishaq a wani dogon hadisi wanda Abujahal ya ce "Ku Quraishawa, haqiqa Muhammad ba komai yake so ba sai aibanta addininmmu, da zagin iyayemmu, da raina hankulammu, gami da wulaqanta allolimmu kamar yadda kuke gani, to wallahi na yi alqawarin daukar dutsen da zan iya dagawa, yana yin sujada na kwankwatse kansa, daga nan zabi ya rage naku, ko dai ko kare ni ko ku miqa ni, albashi in ya so Banu Abdimanaf su yi duk abin da suka ga dama" suka amsa da cewa "Wallahi ba za mu taba miqa ka ba, yi abin da kake son yi!"
.
Alfijir na ketowa Abujahal ya dauki dutse kamar yadda ya yi alkawari, ya je ya zauna yana jiran Annabi SAW, zuwa can anjima Annabi SAW ya fito, ya je ya kama salla, sauran Quraishawa kuma suka bar gidajensu suna jiran su ga abin da Abujahal zai aikata, ko da Abujahal ya dauki dutsen ya nufi Annabi SAW sai kuma ya ja da baya a firgice, duk launinsa ya canja, hannunsa sai kakkarwa yake yi, ya ma jefar da dutsen a qasa, manyan Quraishawa suka dumfare shi suna cewa "Meke faruwa ne Abulhakam?" Ya ce "Na yi niyyar yi masa abin da na gaya muku jiya, sai wani sangamemen raqumi ya fito min, wallahi ban taba ganin wani raqumi da kai, ko wuya ko haqori irin nasa ba, haka ya taso min zai cinye ni".
.
A wani hadisi na Bukhari 1/544 wanda Urwata bnz Zubair ya ce na tambayi Ibn Amr bnl As RA kan mafi tsananin abin da aka yi wa Annabi SAW sai ya ce "Annabi SAW yana cikin salla wajen dutsen Qa'aba sai Uqbata bn Abi Mu'ait ya sanya wani qyalle ya yi mummunan shaqe Annabi SAW har sai da Abubakar RA ya zo ya kama kafadunsa ya finciko shi ya ce " Sai ku kashe mutum don kawai ya ce Allah ne Ubangijina?"
.
MUSLUNTAR HAMZA RA
A watan Zul-Haj qarshen shekara ta 6 kenan, lokacin da Hamza RA wato baffan Annabi SAW kuma dan uwan shan nononsa ya muslunta kenan, dalilin musluntarsa kuwa, Abujahal ne ya sami Annabi SAW a kan dutsen Safa ya yi ta musguna masa amma bai ce masa komai ba, har dai Abujahal ya wawuri wani dutse ya yi wa Annabi SAW rotsi a ka, jini ya yi ta zuba, daga bisani ya yi wucewarsa ya qarisa majalisin Quraishawa a gindin Qa'aba ya yi zamansa, to bararriyar baiwar Abdullah bn Jad'an tana zaune a kan Safan tana kallon abin da yake faruwa.
.
Sa'ilin da Hamza ya dawo farauta da 'yar bakarsa a rataye, sai wannan matar ta kwashe labari ta gaya masa, to a lokacin matashi ne kowa na shakkarsa, nan ya fita zuwa wurin Abujahal a fusace ya yi masa rotsi shi ma da bakar a kai ya ce "Sai ka baci dana bayan ina addininsa?" Na
Post a Comment (0)