ANNABI DA SAHABBANSA //027


*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //027❤️💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

*UMAR BNL KHATTAB YA MUSLUNTA!*
Musluntar Hamza RA ta rikirkita wa Quraishawa lamari, domin su a ganinsu Annabi SAW ne kadai matsalarsu, kuma suna dab ne da su gama da shi kowa ma ya huta, kwatsam sai ga Hamza bn Abdilmuttalib wato baffansa ya bi sahunsa, kwana 3 kacal da musluntar Hamza sai aka ji kuma Umar bn Khattab shi ma ya karbi kalmar shahada, koda yake bayani ya nuna cewa Annabi SAW ne ya yi addu'ar musluntar tasa, domin musulmi sun shiga wani irin hali da suke buqatar taimako, cutarwa ko ta ko'ina, har ya kasance ba za su iya kare kansu ba, don kowa na jikinsa yake gana masa mugunyar azaba.
.
A ruwayar Tirmiziy wace ta qare ga Ibn Mas'ud da Anas bn Malik Annabi SAW ne ya yi addu'a da cewa (Allah ka daukaka muslunci da wanda ka fi so; Kodai Umar bnl Khattab ko Abujahal bn Hisham, sai Allah SW ya zabi Umar bnl Khattab), bayan bincike mai zurfi da malamai suka yi, qarshe dai sun gano cewa tun farko muslunci ya riqa shiga zuciyar Umar RA a hankali-a hankali kafin a qarshe ya sami natsuwa da shi bisa wani dalili.
.
Ko shakku babu Umar RA sananne ne da qarfi ga kuzari da haiba, musulmai kam sun dandana kudarsu a hannunsa, kafin wasu lamura su fara rikice masa, a farko shi mutum ne mai son kiyaye addinin iyaye da kakanni, ga shi mai son fantamawa yadda yake so, to sai dai kuma wannan jajurcewar da musulmai suke yi a kan aqidarsu duk da mummumar takurar da suke fama da ita ta saka shi tunani.
.
Sannan ga wani abin da kowani mai hankali dole ya jujjuya; mai yuwuwa fa musluncinnan ya zama shi ne mafi daukaka a wurin kowa, shi ya sa koda ransa ya baci game da musulmai zuwa wani lokaci kuma sai ka ga ya yi taushi (inji Gazali a Fiqhus sira P92-93) a taqaice dai ana ruwaitowa cewa wani dare ya fita daga makwancinsa zuwa Qa'aba ya lulluba da mayafin Qa'abar a lokacin Annabi SAW yana salla, sai ya fara karanta Suratul Haaqa.
.
Nan ne Umar RA ya saurare shi da kyau, har tsarin Qur'anin ya ba shi sha'awa, bayan ya muslunta ne yake cewa "Wannan lokacin muslunci ya fara shiga zuciyata" sai dai kuma akwai sauran jiqon danqe a jika, masamman zancen addinin iyaye da kakanni, ga rigingimun qabilanci, da gaba da musluncin da aka dauko tun fari, sai wannan ma ya rinjaye shi, har wata rana ya yi niyyar gamawa da Annabi SAW, sai ya ratayo takobinsa ya nufi wurin Annabin, kafin ya isa sai ya yi karo da Nu'aim bn Abdillahil Nahamil Adwiy, wasu malaman suka ce wani ne daga Bani Zuhra ko daga Bani Makhzum ya ce masa "Umar ina kuma aka nufa?" Ya ce "Muhammad nake so na kashe!" Ya ce "To in ka kashe shi ya zaka sami kanka a wurin Banu Hashim da Banu Zuhra?".
.
Umar RA ya ce " Kai ma ina ganin ka riga ka bar addininka" mutumin ya ce "Umar bari na gaya maka abin da ya fi wannan ban mamaki, qanwarka fa da surukinka tuni sun tuba sun bar wannan addinin naka" Umar RA ya canja hanya ya dumfare su a fusace, a lokacin Khabbab bnl Art yana wurinsu yana karanta wasu fallayen da aka yi rubutun Qur'ani wato Suratu Taha a ciki, dama yakan buya ya je ya koya musu, da ya ji motsin Umar RA sai ya labe.
.
Sai qanwarsa Fatima bntl Khattab ta boye takardun, amma sun makara don Umar RA ya riga ya ji muryar Khabbab yana karatun, da shugowarsa ya ce "Wai wani surkulle nake ji ne a nan?" Suka ce ita da mijinta "Banda hirar da muke yi kuma?" Ya ce "Ina ganin kun tuba ne" surikinsa ya ce "Ya kake gani in gaskiya ta bayyana ba a cikin addininka ba?" Nan Umar RA ya far masa ya yi mummunan taka shi, matarsa ta zo ta fincike qafar da qarfi, Umar RA ya dauke ta da mari har sai da fuskar ta kumbura, ita kuma ta ji zafi ta yi kalmar shahada a gabansa.
.
Da Umar RA ya ga ba nasara sai ya ce su ba shi abin da suke karantawa, qanwarsa ta ce sai ya yi tsarki, haka ala-tilas ya yi sannan ya karba ya karanta, Qur'ani ya ratsa zuciyarsa, har ya ce "Ku kai ni wurin Muhammad" da Khabbab ya ji haka sai bul ya fito ya ce "Umar ina maka albishir, ina fata
Post a Comment (0)