ANNABI DA SAHABBANSA //024



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //024❤️💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

*HIJIRA TA 2 ZUWA HABASHA*
Makkawa suna da labarin cewa wasu daga cikin sahabban Annabi SAW sun tafi Habasha, sai kuma suka sami labarin cewa sarkin daular wato Najashiy ya karrama su, nan wutar gabar muslunci da musulmai ta dada balbala a tsakaninsu, suka fuskanci sauran wadan da zaune cikin garin Makka da nau'o'i daban-daban na azaba, har sai da Annabi SAW ya sake umurtarsu da su koma Habasha a karo na biyu, sai dai wannan karon yawansu ya ribanyu sama da na farko, har ya kai 82, wasu suna ganin akwai Ammar, in an hada da shi to yawansu yakai 83 Kenan wato mazan, mata kuma su 18 zuwa 19.
.
Lokacin da Quraishawa suka sakankance da wannan hijirar ta biyu, da kuma irin natsuwar da suka samu a Habashan, sai suka suka yi shawarar cusguna musu a can ma, suka zabi samari majiya qarfi, wato Amr bnl As da Abdullah bn Abi Rabi'a (Sannan ba su muslunta ba) suka aike su da wasu kyaututtuka na gani na fada zuwa wurin Najashiy shi da fadawansa, da suka isa wurin fadawan suka ba su kyaututtukan gami da wasu hujjoji masu gamsarwa wadan da za su yi amfani da su wajen neman iza qeyar sahabbai zuwa inda suka fito, fadawan suka yi alkawarin yin iya qoqarinsu.
.
Amma lokacin da suka iso wajen Najashiy suka ba shi kyautar sai suka yi masa gaisuwar girmamawa suka ce: " Yallabai, Wasu yara marasa ji sun shugo qasarka, wadannan yara sun bar addinin mutanensu sannan sun qi shiga addininka, sai suka qirqiro wani sabon addini suka zo da shi, mu da kai duka ba wanda ya san kansa, don haka muka turo maka manyansu wadan da iyayensu ne, baffanninsu da sauran danginsu don su koma da su gida, don sun fi kowa saninsu da abin da suke zarginsu da shi".
.
Fadawan suka ce "Mai sarauta wannan gaskiya ne, a damqa musu su su koma da su gida" sai dai shi Najashin yana ganin sai an yi tankade da rairaya, ta wajen sauraron duk bangarorin guda biyu, ya sa aka yi masa kiran musulman, su a lokacin sun tsaya kan za su fadi gaskiya komai dacinta Najashiy ya ce "Wai meye haqiqanin wannan addinin da ya sa kuka rabu da addinin mutanenku, kuma kuka qi karbar sauran addinan?"
.
Mai magana da yawun musulmai a lokacin Ja'afar bn Abitalib ne, wato yayan Aliy RA, ya ce "Yallabai, da muna zamanin jahilci ne da gidadanci, sai mu bauta wa gumaka mu ci mushe, mu aikata duk wani alfahasha, mu yanke zumunta, mukan munana wa maqwabci, mai qarfi ya zalunci maras qarfi, haka muke har Allah SW ya turo manzo a cikimmu, mun san dangantakarsa, gaskiyarsa, amanarsa da kamewarsa.
.
"Sai ya kira mu zuwa ga kadaita Allah da bauta masa, gami da qaurace wa abin da muke bauta ma wa mu da iyayenmu na gumaka da duwatsu, ya umurce mu da fadin gaskiya, amana, sada zumunta, kyakkyawar maqwabtaka, da nisantar haram ko zubar da jini, ya hana mu alfahasha shedar zur, gami da cin dukiyar maraya, da yi wa wasu qazafi, ya umurce mu da mu bauta wa Allah shi kadai kuma kar mu hada shi da wani.
.
Ya yi mana umurni da salla, zakka da azumi, muka gasgata shi muka yi imani dashi a kan abin da ya zo da shi na addinin Allah, sai muka bauta wa Allah shi kadai ba mu hada shi da wani ba, muka haramta abin da ya haramta mana gami da halasta abin da ya halasta, don haka sai mutanemmu suka tsane mu, suka riqa cutar da mu, suka takura mu a kan addinimmu, don dai kawai su mai da mu kan bautar gumaka, da aikata munanan ayyuka, lokacin da suka fi qarfimmu suka nemi hana mana addinimmu, sai muka bar qasarmu, muka zabe ka a kan wasu, sabo da tunanin ba za a zalunce mu a wurinka ba"
.
Sai Najashiy ya ce "Ko kana tare da wani abin da yake cewa?" Ja'afar ya ce qwarai kuwa, sai ya fara karanta suratu Maryam, wato (Kaf,Ha,Ya,Ain,Saad) Najashiy ya yi kuka har sai da gemunsa ya jiqa da hawaye, su ma fada-fadan da suke kewaye da shi suka rushe da kuka har suka jiqa littafansu, Najashiy ya ce "Wannan da abin da Isa AS ya zo da shi daga mafita guda ne" ya kalli Amr bnl As ya ce "Wallahi ba zan damqa muku
Post a Comment (0)