ANNABI DA SAHABBANSA //028



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //028❤️💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

Tun lokacin da Umar bnl Khattab RA ya muslunta aka fara sakar wa musulmai mara, a ruwayar bn Abbas (Tarikh Umar bnl Khattab na Inbl Jauziy P6-7) ya ce da Annabi SAW "Wai ba mu ne muke kan gaskiya ko a mutu ko a yi rai ba?" Ya ce "Haka yake, na rantse da wanda raina yake hannunsa kuna kan gaskiya rayuwa ko mutuwa" ya ce "To don me muke buya musu? Na rantse da wanda ya aiko ka da manzonci sai mun fita" ya ce "Muka fita a layi biyu ina gaban daya, Hamza yana gaban dayan, duk qura ta budu masa kamar garin kunu, haka muka qarisa har masallaci, na kalli Hamza na kalli Quraishawa, duk baqin ciki ya maqure su ba su da yadda za su yi, daga wannan ranar Annabi SAW ya sanya min suna Faruq" a ruwayar Bukhari 1/545 musulmai suke cewa "Tunda Umar RA ya muslunta muka sami daukaka".

*MUQADDASHIN QURAISHAWA A GABAN ANNABI SAW*
Tun lokacin da Hamza da Umar RA suka muslunta Quraishawa suka tabbatar da cewa azabtarwa fa ba mafita ba ce, sai dai ba su yi qasa a gwiwa ba, suka tashi wani masamman don ya je wajen Annabi SAW a gyaro ta, za su ba shi duk abin da yake buqata, abin da ba sa so kawai ci gaba da yada muslunci, ba su san cewa duniya da abin dake cikinta inda za a ba wa Annabi SAW ba komai ba ne a wurinsa, wannan bai iya sawa ya dena yin da'awarsa.
"Wata rana Utba bn Rabee'a (shugaba ne), ya miqe a majalisar Quraishawa sannan Annabi SAW yana zaune a gefe shi kadai ya ce "Quraishawa me kuke gani, da ban je na sami Muhammad na yi masa magana kan wasu batutuwa ba? Wata qila ko ya qi karbar wasu zai karbi wasu, sai mu ba shi duk abubuwan da yake so mu dai ya rabu da mu" wannan ya faru ne lokacin da Hamza RA ya muslunta, da suka ga adadin musulmai kullum qaruwa yake sai kawai suka karba.
"Don haka sai Utba ya miqe ya qarisa wurin Annabi SAW ya ce "Dan uwana ka san cewa kana da babban matsayi a cikin dangi, ga lafiyayye dangane, to amma ka zo wa danginka da wani babban abu wanda ka raba kansu da shi, ka raina hankalinsu, ka baci allolinsu da addininsu, ka kafurta duk wanda ya bi addinin iyayensa, yanzu ji nan! Zan yi maka tayin wasu abubuwa kai kuma ka je ka yi tunani wata qila ka amshi wasu daga ciki".
"Annabi SAW ya ce "Abul Waleed, fadi ina jinka" shi kuma ya ci gaba da cewa "In dukiya kake so ya sa ka zo da wannan abin sai mu tara maka ita har ka fi kowa a cikinmu, in kuma wani matsayi kake so sai mu dora ka shugaba a cikimmu ta yadda ba za mu iya yanke komai ba sai da kai, in ma sarauta kake so sai mu nada ka ka zama sarkimmu, in kuma aljani ne yake bullo maka ba ka da yadda za ka yi da shi sai mu nema maka magani, in dukiyarmu za ta qare sai dai ta qare amma sai ka warke, don sau tari akan yi magani kuma a warke" har Utba ya gama Annabi SAW bai tanka masa ba, can sai ya ce "Abulwaleed ka kammala?" Ya ce "Qwarai!" Sai ya ce "To ni ma saurare ni"
"Sai Annabi SAW ya yi bismilla ya fara karanto masa (Alif lam meem) na fussilat, Utba ya yi kasaqe yana jinsa, can dai ya watsa hannunsa a baya ya dogara a kansu yana sauraren Annabi SAW, lokacin da ya kai wurin sujjada ya yi, sannan ya ce "Abul Waleed ka saurare ni? To wannan ce amsarka" sai Utba ya miqe ya nufi wurin mutanensa, suna ganinsa suka ce "Wallahi mutuminku ba da fuskar da ya tafi ya dawo ba" haka dai ya qarisa wurinsu ya sami wuri ya zauna, suka ce "Abul Waleed meke faruwa?"

Ya ce "Na ji wata maganar da wallahi ban taba jin irinta ba, na rantse da Allah ba waqa ba ce, ba sihiri ba, ba bokanci ba, Quraishawa ku saurare ni ku ji maganata, wannan mutumin ku bar shi kawai da abin da ya zo da shi, na rantse muku da Allah wani abu babba zai faru a dalilin abinnan, in Larabawa suka juya masa baya to ku kadai kun isa ku tsaya masa, in kuma Allah ya dora shi a kanku to dama mulkinsa naku ne daukakarsa taku ce za ku fi kowa jin dadi" suka ce "Shi kenan wallahi ya tsafaceka da harshensa!" Ya ce "Wannan ra'ayina ne ku kuma ku yi abin da kuka ga dama".

Lamari
Post a Comment (0)