ANNABI DA SAHABBANSA //029



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //029❤️💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

*AN SAKA WA MUSULMAI TAKUNKUMI*
Abubuwa fa sun kacame wa Quraishawa, masamman cikin makwanninnan guda 4, wadan da Hamza da Umar RA suka muslunta a ciki, sannan an qi sauraron tayin da Quraishawa suka yi wa musulmai, ga Banu Hashim da Banu Abdilmuttalib sun game kai musulmansu da arnansu wajen taimaka wa Muhammad SAW da sauran sahabbansa, wannan a wurinsu ba qaramar matsala ba ce, domin in har suka yi gangancin kashe Annabi SAW to fa daga su har zuriyoyinsu ba wanda zai kai labari, kenan ba wani amfani ga badi ba rai, sai suka koma tunanin wasu hanyoyin cutarwar wadan da ba su kai kisa ba.
"Haka suka taru a yankin Banu Kinana a wani wadi da ake kira Muhassab suka yanke cewa matuqar Banu Hashim da Banu Abdilmuttalib sun hade kai kan kare Muhammad SAW da sahabbansa, to su ma ya kamata a dora musu wani takunkumi mai tsananin gaske, wanda a qarqashinsa ba za a aura musu mace ba, ba kuma za a auro daga cikinsu ba, babu cinikayya a tsakani, ba zaman tare, ba kuma wata ma'amalla, sannan ba wanda zai shiga gidajensu bare ya yi magana da su har sai sun miqo Annabi SAW da kansu don ya fuskanci hukuncin kisa.
"Wannan takunkumi a rubuce aka yi shi kan yarjejeniyar cewa ba za a yi wani sulhu da Banu Hashim ba, kuma ba sani ba sabo har sai sun miqo Annabi SAW, Ibnl Qayyim a Zadul-Mi'ad 2/46 ya lissafo sunayen wadan da aka ce su ne suka rubuta takardar, amma shi ya inganta sunan Bageed bn Amir bn Hashim ne, don shi ne ma Annabi SAW ya yi masa addu'a hannun ya shanye, to bayan an gama rubuta wannan takarda sai aka liqa ta a jikin Qa'aba, Banu Hashim da Banu Abdilmuttalib duk suka juya mata baya in ba Abulahabi ba, wannan takunkumi ya zo daidai da kamawar watan Muharram shekara ta 7 bayan annabci.

*SHEKARA 3 QARAASHIN TAKUNKUMI*
Wannan mamaya da aka yi wa su Banu Abdilmuttalib ta ci gaba har tsawon shekara 3, Quraishawa suka qi yarda wani abinci ya shiga garin Makka sai sun saye shi, da haka suka shiga halin qaqa-ni-kayi, wanda ya kai su ga cin ganyen bishiyoyi, da ganda, kowa na iya jin mata da qananan yara a bayan dutse suna kukan yunwa, ba wani abin dake isa wurinsu in ba a boye ba, ba su iya sayen wani abu in ba a watan Muharram ba don wannan lokacin fatake suna shugowa, duk da haka mutanen Makka suna qara kudin don kar su iya saya.
"Wata rana Hakeem bn Hizam ya dauki alkama don ya kai wa babarsa Khadijah RA, sai Abujahal ya hango shi, ya kuwa tsare shi ya hana shi wucewa, har sai da Abulbukhtariy ya shiga masa kafin ya sami damar wucewa da shi, Abutalib duk da matakan tsaron da aka sanya bai saki jiki da Quraishawa ba, don haka ya riqa sanya Annabi SAW yana kwana a shimfidarsa, don kar mai son kashe shi ya sami dama, in Annabi SAW zai yi barci wani sa'in sai ya sa a yi musayar makwanci da wani daga cikin 'ya'yansa, duk da wannan halin fa Annabi SAW bai daina fita da'awa shi da wasu sahabbansa a lokacin ibada ba.

*AN CIRE TAKARDAR YARJEJENIYAR*
Haka dai aka kwashe shekaru uku cikin wannan halin kamar yadda muka fadi, to a watan Muharram shekara ta 10 bayan annabci nan fa aka dauke takunkumin, wasu cikin dadin rai wasu kuma ba haka ran ya so ba, ja-gaba a cikin sha'anin shi ne Hisham bn Amr bn Lu'ai, dama ya riqa sadadawa da abinci zuwa ga Banu Abdilmuttalib, shi ne ya sami Zuhair bn Abi Umayyal Makhzumiy, mahaifiyarsa Atika bnt Abdilmuttalib ya ce masa "Zuhair, yanzu ranka zai yi maka dadi ka ci, ka sha, amma kawunnanka suna cikin wannan mawuyacin halin?" 
"Sai ya ce "To ya kake so na yi ni kadai? Don wallahi da a ce mu biyu ne da tuni na yage wancan takardar" Hisham ya ce "Ka samu" ya ce "Wa?" Ya amsa "Ni mana" ya ce "Nemo mana na ukun" da jin haka sai ya je wajen Mut'im bn Adiy ya kwankwada shi, ya fado masa zumuncin Banu Hashim da Banu Abdilmuttalib 'ya'yan Abdumanaf, ya yi tir da goyon bayan da ya yi wa Quraishawa a kan wannan zaluncin, shi ma ya nuna cewa shi kadai ne ya ce su 3 ne ya fado Zuhai
Post a Comment (0)