*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*
*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //030❤️💞*
*(C) Baban-Manar Alqasim*
*ZUWA WURIN ABUTALIB NA QARSHE*
Annabi SAW ya ci gaba da zuwa tsakankanin duwatsu yana ibadarsa, koda yake Quraishawa sun kau da kai, wannan ko kusa baya nufin sun miqa wuya, don har yanzu sunanan da muguwar aniyarsu ta ganin bayan muslunci, Abutalib kuma idanunsa a bude suke dare da rana yana jiran ya ga wanda zai matso kusa da Annabi SAW, duk da cewa shekarunsa a lokacin sun ba wa 80 baya, rudani da tashin hankali kullum don gani ya kare Annabi SAW na tsawon lokaci, ko takunkumin da aka yi musu na shekaru duk sun raunana shi, ga ciwon baya irin na girma, don haka ana dauke takunkumin ya kwanta rashin lafiya.
Wannan cuta tasa ta sake yi wa Quraishawa allura, suka ga cewa in fa suka yi sake har ya mutu a wannan halin, daga baya kuma suka yi wa Annabi SAW wani abu to sunansu gaba daya ya gama lalacewa a wurin Larabawa cewa ga abin da suka yi wa dan cikinsu, sai suka sake tasar wasu wakilan suka aika wa Annabi SAW da zammar ba shi abin da ba su taba yi masa tayinsa ba.
.
Tawagar ta qumshi manyan Quraishawa ne, wato Utba da Shaiba 'ya'yan Abu Rabee'a, Abujahal bn Hisham, Umayya bn Khalf da Abu-Sufyan bn Harb, adadinsu dai ya kai kusan 25, suka ce "Abutalib, matsayinka a wurimmu dai ba sai mun gaya maka ba, to gashi girma ya zo maka, kuma muna tsoron ta Allah ta kasance, ka san dai abin dake tsakaninmu da dandankan can, kira shi ka sulhuntamu, kowa ya ciza ya hura, buqatarmu dai ya kame bakinsa kowa ya tafi da addininsa"
.
Abutalib ya sa aka yi masa kiran Annabi SAW, ya ce "Dana! Wadannan su ne manyan jama'arka, abin da ya kawo su shi ne a yi ban gishiri na ba ka manda" daganan ya gaya masa abin da ya taho da su, da cewa za su ba shi duk abin da yake so, shi ma ya rabu da addininsu, daganan kuma ba wanda zai auka wa wani" Annabi SAW ya ce "Da ba ka kira su ga abin da ya fi musu komai ba"
.
Abutalib ya ce "Zuwa ina za ka kira su?" Ya ce "Zan kira su ne zuwa ga kalma daya rak, wace a dalilinta ne Larabawa da ajamawa kab za su rusuna musu" to sai suka daburce, suka rasa abin da za su ce masa, don dama abin da suke gudu ga shi har qari ma za su samu, Abujahal ya ce "Fadi kalmar, mu kuma mu rubanya maka gomanta" ya ce "Ku ce (La'ilaha illal Lah) ku qaurace wa duk wani abin da kuke bauta wa ba Allah ba" suka tafa hannu suna cewa "Abin mamaki, yo kai Muhammad so kake ka mai da alloli su zama qwaya daya jal?"
*SHEKARAR BACIN RAI*
A watan Rajab ne cikin wannan shekarar ta goma bayan annabci cuta ta sha qarfin Abutalib har dai ya ce ga garinku nan, dududu wata 6 ne kacal da dauke takunkumin da aka yi musu, koda yake wasu suna cewa a Ramadan ya rasu, to amma in muka duba cewa an dauke takunkumin a watan Muharram ne, to ba wani zabi kuma da za mu dauka in ba Rajab din ba, koda yake an ce tsakaninsa da Khadijah RA wata 3 ne kacal sai ya fado Ramadan, in muka duba lissafin da kyau za mu ga Rajab din ne dai ba wani zabi.
Abin da ya zo a sahihin Buhari 1/548 shi ne: Lokacin da ajali ya zo wa Abutalib Annabi SAW ya halarci wurin, sannan akwai Abujahal, Annabi SAW ya ce "Baba, ka ce (La'ilaha illal Lah) da wannan kalman ce zan iya tsaya maka gaban Allah" Abujahal ya ce "Ashe Abutalib za ka iya kwadayin barin addinin Abdulmuttalib?" Haka suka yi ta musayar yawu shi da Annabi SAW har sai da kalmarsa ta qarshe ta zama cewa yananan a kan addinin Abdulmuttalib" wannan abin a yi kuka ne ganin kariyar da ya yi wa addini.
Annabi SAW ya yi alkawarin zai nema masa gafara in dai ba hana shi Allah SW ya yi ba, a kan haka Qur'ani suratut Taubah aya ta 113 Allah SW yake cewa ={Bai dace ba ga Annabi da sauran muminai su nema wa mushrikai gafara koda kuwa makusantansu ne bayan ya bayyana musu qiri-qiri cewa su 'yan wuta ne}= a nan ba mu da wata magana mai tsawo da za mu yi, don akwai hadisai ingantattu da Bukhari ya rawaito wadan da suka tantance cewa bai mutu a muslunci ba sannan ceton Annabi SAW ne ma ya sa wutar da zai sh