ANNABI DA SAHABBANSA //031



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //031❤️💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

*AUREN ANNABI DA SAUDAH*
A cikin watan qaramar salla ne wato Shawwal na shekara ta 10 bayan annabci Annabi SAW ya auri matarsa ta farko bayan rasuwar Khadijah RA, wato Sauda bnt Zam'ah, wannan mata RA tana daya daga cikin matan da suka shiga muslunci tun hudowarsa, da ita aka yi hijira ta biyu zuwa Habasha, za mu iya cewa bazawara ce don ta yi auren fari da Sakaraan bn Amr, shi cikin ikon Allah ya muslunta har ma ya yi hijira tare da ita, sai dai Allah bai yi masa dawowa ba, ya cika a can Habasha din, akwai ruwayoyi wajen tantance inda ya rasun, wasu sun ce ya dawo Makka amma bai jima ba.

*FITAR ANNABI SAW ZUWA TA'IF*
Har ila yau cikin wannan shekara ta goma din kuma a watan Shawwal din dai wanda ya zo daidai da qarshen May ko farkon June 619 Miladiya, Annabi SAW ya fita zuwa Ta'if, akwai nisan mil 60 tsakaninta da Makka, haka Annabi SAW ya kwashe wannan nisan a qafa shi kadai in ba bararren bawansa ba wato Zaid bn Harithah, a iya tsawon tafiyannan duk in ya zo wani gari sai ya tsaya ya kira su zuwa ga Allah SW, abin mamaki ba a sami koda mutum guda da ya amsa kiran ba, yana isa Ta'if ya yi karo da wasu 'yan uwa guda 3, wato Abdu-Yalail, Mas'ud da Habib, dukansu dai 'ya'yan Amr bn Umairis Saqafiy ne.
.
Yana samunsu suka sami wuri suka zauna, ya kira su zuwa ga Allah da taimakon muslunci, daya daga cikinsu ya ce "Zan kekketa rigar Qa'aba in dai kai Allah ya aiko" wani kuma ya ce "Wai Allah bai sami wanda zai turo ba ne sai kai?" Na qarshen ya ce "Wallahi ban ce maka uffan, don in da gaske kake kai manzo ne, to ba qaramin hatsari ba ne na maida maka, in kuma qarya kake to ba ka cancanci na amsa maka ba" daganan ne Annabi SAW ya nemi duk su ja bakinsu.
.
Annabi SAW ya kwashe kwana 10 yana tattaunawa da 'yan Ta'if din, ba wani babba wanda bai gana da shi ba, duk dai amsar tasu guda ce, wato "Bar qasarmu ka kama hanyarka" lokacin da ya kamo hanya sai jahilansu da bayinsu suka biyo shi suna zagi, har ma suka yi layi biyu suna yi masa ature, kafin ka ce haka har takalminsa ya jiqe da jini, shi kuma Zaid sai ya fara qoqarin kare Annabi SAW, shi ma suka yi masa rotsi a kai, ba su bar su ba har suka kai su ga gonar Utba da Shaiba 'ya'yan Rabee'a wanda yake mil 3 daga Ta'if, sannan suka koma.
.
To bayan Annabi SAW ya sami wuri a qarqashin inuwar wata rumfar inabi ya zauna ya dan huta, nan ne [Wai] ya yi wannan addu'ar da ta yi fice: "Ubangiji kai nake kai wa raunin qarfina, da qarancin dubarata, da yadda mutane suke qasqanta ni, kai ne mafi tausayin masu tausayi, kai ne Ubangijin masu rauni, kai ne Ubangijina, ga wa ka miqa ni? Ga manisanci ne wanda zai qi ni ko abokin gaba wanda zai mallaki lamarina? To indai baka yi fushi da ni ba zan damu ba, sai dai rangwamenka shi ya fiye min, ina neman tsarinka da hasken fuskarka da ka haskaka duffai, lamuran duniya da lahira suka gyaru a dalilinsa da kada ka yi fushi da ni, qoqarina yana gareka har ka amince, ba wata dabara ko qarfi sai a gareka"
.
Lokacin da 'ya'yan Rabee'a suka ganshi sai 'yan zumuncin suka motsa, nan suka kira wani Banasaren bawansu da ake kira Addas suka ba shi inabin suka ce ya kai wa Annabi SAW, yana karba ya ce "Bismillah" ya tura a baka, Addas ya ce "Amma fa mutanen garinnan ba su fadin wannan maganar" sai Annabi SAW ya tambaye shi "Kai daga ina kake, kuma meye addininka? Sai ya amsa masa da cewa "Daga Nainawa nake" ya ce "Oooo! Garin bawan Allannan Yunus dan Matta?" Ya ce "Ka san wani abu game da shi ne?" Annabi SAW ya amsa masa da cewa "Ai dan uwana ne, ni da shi duka annabawa ne" nan Addas ya zauna ya juyo qafa da hannu zuwa ga Annabi SAW.
.
'Ya'yan Rabee'a na hango shi daya ya ce wa dayar "Shi kenan wallahi ya bata maka bawa!" Yayin da Addas ya qaraso sai suka ce masa "Wai me kenan ka yi?" Ya ce "Yallabai, ba wani abin da ya fi mutuminnan a bayan qasa, ya gaya min wata maganar da ba mai fadinta sai annabi" suka ce masa "Wai kai me
Post a Comment (0)