SHIN KA NA KYAUTATA WALLAFAR LITTAFINKA?



SHIN KA NA KYAUTATA WALLAFAR LITTAFINKA?

A ranar Alkiyama za a zo da littafan ayyukan bayi, a bama kowa littafinsa a hannunsa don ya karanta da kanshi abubuwan da ya aikata, wani ya karba da dama wani da hagunsa, Ka kyautata wallafar littafinka da abin da kake son ka gani a ranar da kuɗi da 'ya 'ya ba za su yi amfani ba! Shin ka na tuna cewa duk abin da kake aikatawa yana nan a na rubuceshi cikin littafin nan naka?

Kai ne bidi'oi, mu'amala da riba, luwadi, zinace zinace, ha'inci da yaudara, karya, kashe rai, saka yan uwanka musulmai a mawuyacin hali, zalumci, sata, fashi da makami, fyade wa 'ya 'yan jama'a, tozarta amanar iyalanka, wasa da sallah, bin bokaye dss dan Allah ina za ka je da wadannan laifuka???

Dan uwa yanzu ka yarda ka amintu mutuwa ta sameka a wannan halin da kake ciki? 

Ba ki da aiki sai bin bokaye da yan tsibbu, ke dai ki mallake miji daga ke sai yayanki, madigo, gulma da annamimanci, ke ce karya da makirci don ki kuntata wa kishiyarki, ke ce yaudara, cin amana, zinace zinace, komai ya sameki ba za ki yarda da kaddara ba ai wance ce, da aurenki amma kina bin wasu maza a waje, ba ki da aure amma duk wata ma'amala ta aure tana shiga tsakaninki da mazan wasu, tallata kanki da tsiraicinki sune sana'arki, kin dauki rayuwar bariki wai ke a dole wayayyiya, babu banbanci tsakaninki da Ungozi sai a suna! Haba yar uwa yanzu kin yarda kin aminta mutuwa ta riskeki a kan wannan ayyukan naki?

Yanzu yan uwa musulmai wane aiki ne muka bar ma wadanda ba musulmai ba???

Yan uwa ina za mu je da irin wadannan zunuban? Mai zai sa bala'oi da masifu ba za su dabaibayemu ba?? Yaushe za mu gyara dabi'unmu da halayyanmu? Shin sai mutuwa ta riske mu sannan???

Allah Madaukaki Ya ce: 

"وَوُضِعَ الْكِتَابُ فَتَرَى الْمُجْرِمِينَ مُشْفِقِينَ مِمَّا فِيهِ وَيَقُولُونَ يَا وَيْلَتَنَا مَالِ هَٰذَا الْكِتَابِ لَا يُغَادِرُ صَغِيرَةً وَلَا كَبِيرَةً إِلَّا أَحْصَاهَا ۚ وَوَجَدُوا مَا عَمِلُوا حَاضِرًا ۗ وَلَا يَظْلِمُ رَبُّكَ أَحَدًا"

(الكهف :49) 

"Kuma a ka aza littãfin ayyuka, sai ka ga mãsu laifi sunã mãsu jin tsõro daga abin da ke cikinsa, kuma sunã cẽwa "Kaitonmu! Mẽne ne ga wannan littãfi, bã ya barin ƙarama, kuma bã ya barin babba, fãce yã ƙididdige ta?" Kuma suka sãmi abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka bã Ya zãluntar kõwa".

Lallai Allah mai gafara ne ga wanda yayi ingantacciyar tuba, kuma wallahil azeem Shi mai tsananin azaba ne ga masu ta'addanci da wuce iyaka.

#Zaurandalibanilimi

TELEGRAM
https://t.me/Zaurandalibanilimi

INSTAGRAM
https://instagram.com/zaurandalibanilimii?igshid=emf6f90ssc24
Post a Comment (0)