_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_
_*ANNABI DA SAHABBANSA // 20*_
.
```HANYOYIN DAQILE DA'AWA```
_Yayin Da Quraishawa Suka Ka Ga Alamar Cewa Annabi Saw Bai Da Niyyar Sauya Da'awarsa Ta Kowace Hanya, Sai Suka Sake Tunani, Suka Tsara Wasu Hanyoyi Na Daqileta:-_
_1) Ta Hanyar Isgili, Qasqantarwa, Qaryatawa Da Kunyatarwa, Sun Yi Haka Ne Don Su Wulaqanta Musulmai, Su Karya Lagonsu, Sai Suka Faro Ta Kan Annabi Saw Inda Suka Soke Shi Da Hauka, Suka Ce ={Wanda Aka Saukar Maka Da Qur'ani Tabbas Mahaukaci Ne Kai}= Hijr6, ={Sun Yi Mamakin Da Mai Gargadi Ya Zo Musu, Suka Ce: Wannan Maqaryacin Matsafi Ne}= Swad4._
.
_2) Bata Koyarwar Addinin Da Qirqirar Rudani Ta Wajen Yada Qarairayi, Da Baza Maganganu Barkatai Yadda Za Su Ga Qarshen Da'awar Musluncin, Suka Ce Qarairayin Mutanin Da Ne Ake Gaya Masa Safiya Da Maraice Yana Rubutawa, Duba Furqan5, A Kan Annabi Saw Kuma Suka Ce: Wannan Wani Irin Manzo Ne Da Yake Cin Abinci Yana Yawo A Kasuwanni? Duba Furqan8._
.
_3) Bijire Wa Qur'ani Ta Wajen Kawo Wasu Tatsuniyoyi Wadan Da Za Kawar Da Su Daga Sauraron Qur'ani, Da Haka Ne Nadr Bnl Harith Ya Tafi Hirah Ya Koyo Qarairayin Sarakunan Iran Da Tatsuniyoyin Rastom, Ta Yadda In Annabi Saw Ya Zauna Wajen Ba Da Ilimi Da Tunatarwa Gami Da Tsoratarwa Daga Kamun Allah Sw, Sai Shi Kuma Nadr Ya Biyo Baya Yana Cewa: Wallahi Muhammad Bai Fi Ni Iya Labari Mai Dadi Ba, Sai Ya Fara Rabaran Sarakunan Iran Ya Ce: To Da Me Ya Fi Ni?_
.
_4) Sulhu: Sun Nemi Musulmai Su Zauna Da Su Kan Teburin Shawara Don Tattauna Yadda Za A Yi Raba Daidai Kowa Ya Sauka Daga Wasu Aqidojinsa, Suka Ce Annabi Saw Ya Bar Wasu, Su Ma Su Janye Daga Wasu, A Ruwayar Ibn Jarir Da Tabarani Sun Nemi Muhammad Saw Ya Bauta Wa Allolinsu Na Shekara, Su Ma Su Bauta Wa Nasa, A Wata Ruwaya Ta Abd Bn Humaid Sun Ce: Da Ka Yarda Da Allolimmu Da Mun Bauta Wa Ubangijinka. Tafheemul Qur'an 4/8._
.
_A Wata Ruwayar Ma Ta Ibn Is'haq Ya Ce: Wata Rana Annabi Saw Yana Dawafi Sai Aswad Bn Abdulmuttalib Bn Asad Bn Abdil Uzza, Walid Bnl Mugira, Umayya Bn Khalf Da Ass Bn Wa'il Assahamiy Wadan Da Su Ne Masu Fadi A Ji A Cikin Mutanensu, Suka Same Shi Suka Ce: Muhammad Zo Mu Bauta Wa Abin Da Kake Bauta Wa, Kai Ma Ka Bauta Wa Namu, Idan Naka Ne Daidai To Mun Yi Dace Kenan Da Kai, In Kuma Namu Ne Daidai To Kai Ma Ka Tsinci Dami A Kala, Dalilin Saukar Qulya Kenan Gaba Dayanta._
.
```MAFARIN TAKURA WA MUSULMAI```
_Duk Lokacinnan Da Aka Kwashe Na Tsawon Shekara 4 Da Fara Saukar Wahayi Kafurai Ba Su Wuce Wadannan Hanyoyi Da Muka Zayyana A Sama Ba, Sai Dai Sun Fara Da Wannan Ne, In Suka Dan Jima Suka Ga Kwalliya Ba Ta Biya Kudin Sabulu Ba Sai Su Canja Wani, Da Haka Har Suka Kai Ga Yi Wa Annabi Saw Tayin Musayar Bauta, Abin La'akari Ba Wai Su Iya Barin Bauta Wa Gumakan Na Tsawon Shekara Ko Annabi Saw Ya Bauta Wa Allolin Nasu Ba, Ta Ya Za Su Iya Kawar Da Wannan Baqin Girman Kan Su Bauta Wa Allan Da Annabi Saw Ya Zo Da Shi Har Na Tsawon Shekara? A Qarshe Dai Buqatarsu Ita Ce Su Hana Yaduwar Wannan Addini Na Muslunci Ko Ta Halin Qaqa._
.
_To Sai Suka Sake Kafa Wani Kwamiti Mai Mambobi 25, Duk Dai Quraishawan Ne, Qarqashin Jagorancin Abulahab, Bayan Tunani Da Shawarwari Sai Wannan Kwamiti Ya Dauki Wani Tsattsauran Mataki Kan Annabi Saw Da Sahabbansa Ra, Ta Wajen Zage Dantse Don Yaqar Muslunci, Da Cutar Da Annabi Saw, Da Azabtar Da Duk Wanda Ya Shiga Addininsa Ta Yadda Zai Fuskanci Nau'o'i Daban-daban Na Azaba Har Ya Saduda Ta Canja Ra'ayi._
.
_Ba Shakka Zartar Da Irin Wannan Mataki A Kan Musulmai, Masamman Masu Rauni A Cikinsu Abu Ne Mai Matuqar Sauqi, Amma Annabi Saw Lura Da Irin Halittar Da Allah Sw Ya Yi Masa, Da Kasancewarsa Manzo Ba Abin Da Za Su Iya, Masamman Ma Yadda Yake Gaban Baffansa Abutalib, Irin Su Abutalib A Makka Wannan Lokacin Yatsun Hannu Suke Qirga Su, Na Farko Yana Da Haiba Sannan Kowa Yana Ganin Girmansa, Ba Wani Wanda Zai Yi Gangancin Isa Inda Ba Ya So, Shi Ya Sa Abin Ya Rikice Wa Quraishawa Gaba-dayansu, Suka Rasa Yadda Za Su Yi Da Shi._
_*✍🏼Baban Manar Alqasim*_
