_*⚖ZAUREN MARKAZUS SUNNAH⚖*_
_*ANNABI DA SAHABBANSA // 017*_
.
_A Baya Mun Gano Cewa Makka Cibiya Ce Ta Addini A Wajen Larabawa, Wadan Da Suke Kula Da Dakin Kuma Su Ne Jagorori Wajen Bautar Gumakan Dake Daki Mai Alfarma, Don Haka Kawo Gyara A Wannan Wuri Dole Ya Yi Dan Karen Wahala, Sabanin A Ce Wani Wuri Ne Na Larabawan Ba Nan Ba, Ba Shakka Lamarin Yana Buqatar Jajurcewa Ta Yadda Masifu Da Wahalhalu Ba Za Su Gigita Mutum Ba, Wannan Yana Daya Daga Cikin Hikimar Da Ta Sa Dole Sai Dai A Fara Yin Kira Zuwa Ga Musluncin A Boye, Don Kar Makkawan Su Yi Wa Lamarin Wani Irin Kallo._
.
_Wadan Da Annabi Saw Zai Fara Kawo Musu Lamarin Su Ne Wadan Da Suka Fi Kowa Kusanci Da Shi, Kamar Iyalinsa Da Abokansa, Su Din Ne Kuwa Ya Fara Kira Zuwa Ga Muslunci, Sai Kuma Wadan Da Yake Ganin Akwai Alamun Alkhairi Tare Da Su, Cikin Wadan Da Suka Yi Masa Kyakkyawar Fahimta Shi Ma Ya Yi Musu, Ya San Gaskiyarsu Da Kyawawan Dabi'unsu, Wadannan Mutanen Su Ne Suka Amsa Masa, A Zahiri Ba Su Da Wani Kokwanto Game Da Manzancinsa Ko Gaskiyar Lamarinsa, Su Ake La'akari Da Su A Matsayin Wadan Da Suka Riga Kowa Karbar Shiriya._
.
_Cikinsu Akwai Uwar Muminai, Wato Khadijah Bnt Khuwailid Ra, Sai Kuma Bararren Bawansa Wato Zaid Bn Haritha Bn Shurahbil Alkalbiy, -wannan An Taba Kama Shi Aka Mai Da Shi Bawa, Khadijah Ra Ta Mallake Shi, Daga Bisani Ta Yi Wa Annabi Saw Kyautarsa, A Lokacin Babansa Da Baffansa Suka Zo Tafiya Da Shi Wajen Danginsa Amma Sai Ya Yi Qememe, Ya Zabi Ya Zauna Tare Da Annabi Saw, Ganin Haka Sai Annabi Saw Ya Mai Da Shi Dansa Yadda Har Gadonsa Zai Iya, Aka Fara Kiransa Zaid Bn Muhammad, Da Muslunci Ya Bi Jiki Sai Kuma Aka Hana- Na Ukunsu Shi Ne Aliy Ra._
.
_Shi Aliy Ra A Lokacin Yaro Ne, Annabi Saw Ya Karbo Shi Daga Abutalib Don Ya Zauna A Hannunsa, Bayansa Sai Abokinsa Na Kusa Tun Yaranta, Wato Abubakar Ra, Wadannan Tun Ranar Da Annabi Saw Ya Zo Da Annabci Suka Karba Hannu Bibbiyu Kuma Suka Yi Imani Da Shi, Abubakar Ra Mutum Ne Mai Sauqin Hali, Mai Dadin Rai Ga Sauqin Mu'amalla, 'yan Uwansa Sukan So Zama Da Shi Don Yana Da Ilimi Kuma Ga Sanin Kan Kasuwanci, Wannan Damar Ce Ya Samu Shi Ma Ya Fara Nuna Musu Hasken Musluncin, Cikin Wadan Da Ya Amince Da Su, Akwai Usman Ra, Wanda Yake Da Sunan Babansa, Masana Suna Cewa Sunan Abubakar Ra Na Asali Abdullah Bn Usman._
.
_Wadannan Da Muslunci Ke Ji Da Su, Ake Yi Musu Laqabi Da Wadan Da Aka Yi Musu Albashir, Kuma Aka Fito Da Sunansu A Matsayin Fitattun Da Za A Tsayar Da Dayansu A Matsayin Khalifa Bayan Umar Ra Duk A Hannun Abubakar Ra Din Ne Dai Suka Sami Hasken Muslunci, Kamar Dai Shi Usman Bn Affan Ra, Zubair Bn Awwam Al'asdiy Ra, Abdurrahman Bn Auf Ra, Sa'ad Bn Abi Waqqas Ra Da Talha Bn Ubaidillah Attaimiy Ra, Ba Shakka Wadannan Su Ne A Sahun Farko Wajen Shiga Muslunci Sai Kuma Wadan Da Su Kuma Allah Sw Ya Shiryar Bayan Wadannan Irin Su: Bilal Bn Abi Rabah Alhabashiy, Abu Ubaida Amir Bnl Jaraj Daga Bnl Harith, Abu Salama Bn Abdil Asad, Arqam Bn Abil Arqam Almakhzumiyan._
.
_Sai Kuma Usman Bn Maz'un Da 'yan Uwansa Qudama Da Abdullah, Sai Ubaidata Bnl Harith Bnl Muttalib, Sa'id Bn Zaid Al'adwiy Da Matarsa Fatima Bntl Khattab 'yar Uwar Umar Ra, Khabbab Bnl Art, Abdullah Bn Mas'udil Huzaliy Da Dai Sauransu, Dukkan Wadannan Suna Cikin Wadan Da Ake Kiransu Da Marigaya Shiga Muslunci, Gaba Dayansu Quraishawa Ne, Ibn Hisham 1/245-262 Yana Cewa Sun Wuce 40, Duk Sun Shiga Muslunci, Annabi Saw Yakan Gana Da Su A Boye, Ya Sanar Da Su Addininsu, Don A Lokacin Da'awa Ba Ta Watsu Ba, Da Guda-guda Ake Yi, Akwai Maza A Cikinsu Da Dama, Sai Mata Daidaiku._
.
_Wahayi A Lokacin Ya Ci Gaba Da Sauka Bayan Saukar Muddatthir, Sai Dai Ayoyin Galibinsu Da Surorin Za Ka Taras Gajeru Ne, Masu Shiga Rai, Wadan Da Suke Wanke Zuciya, Su Nesanta Mutum Daga Kwadayin Duniya, Su Sifanta Masa Aljanna Da Wuta Kamar Yana Ganinsu Quru-quru, Su Kwashi Hankalin Mutum Zuwa Wata Duniyar Yadda Zai Tabbatar Wa Kansa Cewa Da Fa Ana Cikin Bata Ne Babba, Daga Nan Ne Aka Fara Saukar Da Sallah Raka 4, Biyu Da Safe Sauran Biyun Da Maraice, Mukhtasar Siratir Rasul Abdullahin Najdiy P88, Ibn Hisham 1/247 Ya Ce: Annabi Saw Da Sahabbansa Sun Riqa Boye Sallarsu A Tsakanin Duwatsu Har Abutalib Ya Taba Kama Annabi Saw Da Aliy Ra Wata Rana Suna Sallah Ya Yi Musu Magana, Amma Da Ya Ji Yadda Abin Yake Sai Ya Ce Su Ci Gaba Kawai._
.
_*✍🏼Baban Manar Alqasim*_
