HUKUNCIN ADDU'A TSAKANIN HUDUBAR JUMA'A TA FARKO DA TA BIYU



HUKUNCIN ADDU'A TSAKANIN HUDUBAR JUMA'A TA FARKO DA TA BIYU

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum malam ya gida ya kuma dawainiya dafatan kowa lfy Allah yasa haka ameen, mal ina da tambaya ne akan  halaccin addu'a da akeyi tsakanin huduban farko da na karshe,  Allah yasaka alkhairi.

*AMSA*👇

Wa alaikum assalam To dan'uwa Annabi s.a.w. yana cewa: " A ranar juma'a akwai wani lokaci wanda babu wanda zai dace da shi, ya roki Allah a lokacin , face sai ya amsa masa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 893.
Malamai sun yi sabani game da wannan lokacin zuwa wajan zantututuka arba'in, kamar yadda Ibnu Hajar ya hakaito a Fathul-bary, 2\419, daga cikin wadannan maganganun akwai cewa : tsakanin hudubobin juma'a guda biyu lokacin yake fadowa.
Don haka wasu malaman suke ganin mustahabbancin yin addu'a tsakanin hudubobi biyu, saboda musulmi zai iya dacewa da wancan lokacin mai falala.

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)