HUKUNCIN WANDA YA RISKI ZAMAN TAHIYA A SALLAR JUMA'AH ?



HUKUNCIN WANDA YA RISKI ZAMAN TAHIYA A SALLAR JUMA'AH ?

*TAMBAYA*❓

Assalamu Alaikum Malam, nine nazo juma'a a makare sai natararda zaman tahiyya, shin in imam ya sallame raka'o'i 2 zanyi ko 4?

*AMSA*👇

Akwai fahimta guda 2 akan haka:

Nafarko= Mazhabin IMAM ABU HANIFA da IBNU HAZMIZ ZAHIR- suna ganin in har yasami imam kafin yayi sallama koda a tahiyyane to raka'o'i 2 na juma'a zai kawo, HUJJARSU akan haka shine Hadisin ABU HURAIRA R/A
٤٨ - ‏[ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ : ‏] ﺇِﺫﺍ ﺃُﻗِﻴﻤَﺖِ ﺍﻟﺼَّﻼﺓُ، ﻓﻼ ﺗَﺄْﺗُﻮﻫﺎ ﺗَﺴْﻌَﻮْﻥَ، ﻭﺃْﺗُﻮﻫﺎ ﺗَﻤْﺸُﻮﻥَ، ﻋَﻠَﻴْﻜُﻢُ ﺍﻟﺴَّﻜِﻴﻨَﺔُ، ﻓَﻤﺎ ﺃﺩْﺭَﻛْﺘُﻢْ ﻓَﺼَﻠُّﻮﺍ، ﻭﻣﺎ ﻓﺎﺗَﻜُﻢْ ﻓﺄﺗِﻤُّﻮﺍ .
ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( ٢٥٦ ﻫـ ‏) ، ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ٩٠٨ • ‏[ ﺻﺤﻴﺢ ‏] • ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( ٩٠٨ ‏) ، ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( ٦٠٢ ) •
Wato= "abinda kuka tarar kusallata abinda ya subuce muku kuma kuma kuciko" sukace ai abinda yakubce raka'o'i 2 ne don haka su za'a kawo.

NABIYU= JAMHURIN MALAMAI kuma sun tafi akan tunda bai samu ruku'i sai tahiya to bai sami raka'a ko ɗaya ba, don haka bai sami juma'a ba, don haka raka'o'i 4 na azahar zai kawo, HUJJARSU shine Hadisin ABU HURAIRA
٧ - ‏[ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ : ‏] ﺃﻥَّ ﺭَﺳﻮﻝَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﷺ ﻗﺎﻝَ : ﻣَﻦ ﺃَﺩْﺭَﻙَ ﺭَﻛْﻌَﺔً ﻣِﻦَ ﺍﻟﺼَّﻼﺓِ، ﻓﻘَﺪْ ﺃَﺩْﺭَﻙَ ﺍﻟﺼَّﻼﺓَ .
ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( ٢٥٦ ﻫـ ‏) ، ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ٥٨٠ • ‏[ ﺻﺤﻴﺢ ] •
Lafazin MUSLIM kuma
[ ﻋﻦ ﺃﺑﻲ ﻫﺮﻳﺮﺓ : ‏] ﻣَﻦ ﺃﺩْﺭَﻙَ ﺭَﻛْﻌَﺔً ﻣِﻦَ ﺍﻟﺼَّﻼﺓِ ﻣﻊ ﺍﻹﻣﺎﻡِ، ﻓﻘَﺪْ ﺃﺩْﺭَﻙَ ﺍﻟﺼَّﻼﺓَ .
ﻣﺴﻠﻢ ‏( ٢٦١ ﻫـ ‏) ، ﺻﺤﻴﺢ ﻣﺴﻠﻢ ٦٠٧ • ‏[ ﺻﺤﻴﺢ ‏] • ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ‏( ٥٨٠ ‏) ، ﻭﻣﺴﻠﻢ ‏( ٦٠٧ ) •
Wato= "wanda yatararda raka'a ɗaya tareda imam to yatararda sallan"
KISHIYAR FAHIMTAR ( ﻣﻔﻬﻮﻡ ﺍﻟﻤﺨﺎﻟﻔﺔ ) na hadisinnan shine
ﻭﻣﻦ ﻟﻢ ﻳﺪﺭﻙ ﺭﻛﻌﺔ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻟﻢ ﻳﺪﺭﻙ ﺍﻟﺼﻼﺓ
Wato= Wanda bai tararda raka'a ko ɗaya ba to bai sami sallan ba, tunda bai samu juma'ar ba to azahar zaiyi wato raka'o'i 4,
Yayinda shi kuma ABU HANIFAH bai yarda da MAFHUMUL MUKHALAFAH ba,
SHEIKH MUHD IBN ABDIL-MAQSUD ya rinjayarda maganar jamhuran Malamai nabiyan raka'o'i 4 na azahar tunda bai sami juma'a ba.

ALLAHU A'ALAM.

via : Sheikh Abubakar BN Mustafa Biu

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)