HUKUNCIN MAI JANABA YA KARANTA ALQUR'ANI?
*TAMBAYA*❓
Allah ya kara wa malam lafiya ameen. Malam menene hukuncin Wanda yakaranta wasu surori daga cikin alqur'ani alhalin yana cikin janaba wato bai tsarkake jikin sa ba?
*AMSA*👇
Wa'alaikumus Salám, Mafi yawan malaman Fiqhu daga Mazhabobin nan huɗu sun tafi a kan haramcin karanta Alqur'ani ga mai janaba ko da kuwa da ka ne.
Imamut Tirmizhiy ya bayyana cewe: "Wannan fahimtar ita ce maganar mafi yawan ma'abota ilimi daga cikin Sahabbai da Tabi'ai, da waɗanda suka biyo bayansu, kamar su Sufyanut Thauriy, da Ibnul Mubárak, da Assháfi'iy, da Ahmad da Ishaq". Sunanut Tirmizhiy (1/195).
Haka nan Alkásániy ya ce: "Ba ya halasta ga mai janaba ya yi karatun Alqur'ani a wurin gamayyar malamai". Badá'i'us Saná'i'i (1/37).
Shaikhul Islam Ibn Taimiyya ya ce: "Haka nan mai janaba ba zai karanta Alqur'ani ba a fahimtar mafi yawan malaman mazhabobin Fiqhu guda huÉ—u, da ma wasunsu, kamar yadda Sunnah ta yi nuni a kan haka".
Duba Majmú'u Fataawá na Ibn Taimiyya (17/12).
Saboda haka Æ´ar uwa ba ya halasta ga mai janaba ya karanta Alqur'ani har sai ya yi tsarki, wanda kuma ya yi hakan ya yi kuskure a bisa fahimtar mafi yawan malamai. Kuma wannan ita ce Fatawar da Lajna suka bayar a mujallad na biyar shafi na 429.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Yaku Yan'uwa masu albarka Ku taya mu isar da wannan sakon ta hanyar SHARING wasu da yawa zasu amfana.
Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177