IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA



IDDAR MATAR DA BA TA YIN HAILA DUK WATA

                               *TAMBAYA*❓

Malam idan ya zama mace ba ta yin haila sai duk bayan wata uku, yaya idarta za ta kasance ?

                                  *AMSA*👇

To malam dole ne, sai ta yi jini uku kamar yadda Hanafiyya suka fada, ko kuma tsarki uku kamar yadda Malikiyya suka tafi akai, ko da kuwa duk shekara take yin haila sau daya, saboda Allah madaukaki ya rataya idda ne da samuwar jini, kamar yadda yake cewa a cikin suratul Bakara aya ta: 228 "Kuma matan aka saka, to za su jira tsawon jinane uku"

*_DON HAKA DUK TSAWON LOKACIN DA ZA TA ZAUNA TO DOLE SAI TA JIRA SU, KAMAR YADDA AYAR TAKE NUNAWA._*

Allah ne mafi sani.

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Ya kai dan'uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yaɗa ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci.
_Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah._

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)