HUKUNCIN SAKA HOTON ANGO DA AMARYA A KATI KO KALANDA (pre-wedding pictures)
:
*TAMBAYA*❓
:
Mene ne hukuncin saka hoton ango da amarya a kalanda ko kati tare da ayoyin Alqurani ko
hadisan Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama a rarrabawa mutane?
:
*AMSA*👇
:
Yin wadannan sabawa Shariar Allah ne karara, da wulakanta ayoyin Alkurani da hadisan Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama, da kuma jahiltar addinin Musulunci tare da sabawa kyawawan al`adunmu na gari da muka gada.
Kuma wani babban abin bakin ciki ma shi ne yadda za ka ga irin waÉ—annan hotunan masu dauke da sunan Allah ko hadisan Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama an zubar da su a bola (juji) ko kuma wurin kazanta bayan an
gama bikin . Wannan yana nuna irin rashin kishin wasu mutanenmu, ta yadda za ka ga an buga hoton ango da amarya ta yi ado cikin gwalagwalai da kaya masu bayyana siffar jikinta. Tare da haka, wasu ma har lambar wayarsu suke sanyawa a jikin hoton wanda wannan zai iya ba da kofar wata fitina ta samu.
Da fatan Allah ya shirye mu baki É—aya.
Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaÉ—a wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, _Amma don girman ALLAH kada ku kwafa ku goge wani abu daga ciki. Kuji tsoron ALLAH
Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177