MENENE HUKUNCIN YIN SALLAH A GABAN LIMAN A WAJAN MASALLACI ?

TAMBAYA❓


MENENE HUKUNCIN YIN SALLAH A GABAN LIMAN A WAJAN MASALLACI ?

ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ .
AMSA:👇

 Asali Sallar jam'i shine Mamu ya kasance A bayan liman, Malamai Sunyi Sabani akan sallar wanda yayita Agaban liman, Mafi ingancin Zancen shine ta Inganta idan Akwai uzuri.

Shaikul Islam Ibnu Taimiyyah Rahimahullahu yace: Sallah agaban liman akwai zantuka guda uku na Malamai akai..

1- Ta inganta kai Tsaye, duk da sunce Makaruhine, Shine zance shaharre a Mazhabar Malikiyya.

2- Bata Ingantaba, Kamar Mazhabar Hanafiyyah, da Shafi'iyyah, da Ahmad.

3- Ta inganta idan akwai Uzuri, Kamar babu sauran gurin da mutum zaiyi Sallar sai gaban liman din, Saiya zama yin Sallar agaban Liman shine Yafi Alkhairi akan qin yin Sallar alokacin.
Wannan shine zancen wasu malamai, shine Mazhabar Imamu Ahmad da waninsa, shine mafi Adalcin zance shine yafi hujjah Mai qwari, domin barin shiga gaban liman Maqurarsa shine wajabcin barin hakan, su kuma wajibai suna gushewa idan aka samu uzuri, koda wajibine a asalin sallah, da rasa jam'i gwara rasa wajibi, Saboda haka wajabcin Abunda mutum yakasa yana faduwa agareshi, na Tsayuwar Sallah, da karatu, da tufafi, da Tsarki, da sauransu.
Fatawa Kubra ( 2 / 331 - 333 ).

Saboda haka Bai halatta yin Sallah Agaban liman ba, idan Mutum yai sallah agaban liman saiya sake sallah, saidai idan Akwai uzuri Masallaci babu sauran filin dazaka iya tsaiwa damansa ko hagu dinsa.
Kamar Yanda Ibnu Usaimeen Yafada acikin Maj- Mu'u fatawa dinsa (13 / 44 ).

Wallahu A'alamu.

Ku kasance damu domin ilimintarwa, Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)