SALLAR TASBIHI



SALLAR TASBIHI

To da yake É—alibi ne ni, ba wani sani gare ni ba. Amma dai na ga bayanan malamai a kanta.

Siffarta
Raka'a huɗu kowacce da fatiha da sura gajera. Kamar dai yadda malam ya yi bayani a bidiyon. Sannan bayan karatun fatiha da na sura, sannan mutum zai yi tasbihi goma sha biyar; sannan idan ya yi ruku'u ya yi guda goma; idan ya ɗago ya yi goma; idan ya yi sujjada ya sake yin goma; idan ya ɗago ya yi wata goman; idan ya koma ya sake goma; idan ya ɗago ya ƙara goma. Kowacce raka'a jumulla guda saba'in da biyar kenan.

HUKUNCINTA
Malamai sun tattauna a kan ingancinta, akwai waɗanda suka inganta ta; wasu kuma suka kyautata ta; wasu suka raunana ta; wasu kuma suka ce ƙarya aka jingina wa Annabi (S.A.W). Ibnul Jauzi ya kawo a cikin littafinsa (Almaudu'at).

Wanda suka inganta ta, sun yi duba da falalar da ke cikinta. Amma sun kansu sun gamsu hadisin shazzi ne, ma'ana ya ci karo da ingantattun hadisai.

Imamu Tirmizi ya ce "An rawaito hadisi ba ɗaya ba biyu ba daga Annabi (S.A.W) amma duk babu wanda ya inganta." Imamu Nawawi ya naƙalto daga Uƙaili cewa "Babu wani abu ya inganta daga Annabi (S.A.W) a kan batun sallar tasbihi." Haka Ibnul Arabi ya kawo. Imamu Nawawi ya hakaito maganganun a cikin Sharhul Muhhazab.

"Magana ta gaskiya a kan batun sallar tasbihi, duk hanyoyin da aka rawaito ta ba su inganta ba. Sannan bayan Imamu Ahmad da ya rawaito, su Abu Hanifa; Malik da Shafi'i ba a taɓa ji sun zantar da ita ba." Hakan mai littafin Alfuru'u ya naƙalto.

Muhammad Bn Salih Al'outhaymeen ya ce "Abin da ya kamata a rinjayar shi ne ba ta inganta ba, saboda dalilai kamar haka:
1- Asali a kan ibada shi ne hani, sai idan dalili ya tabbata a kan shar'ancinta.
2- Hadisin akwai idɗirabi (tufka da warwara) a cikinsa, riwayoyinsa sun zo da saɓani.
3- Malamai ba su sa ta cikin mustahabbi ba, Ibn Taimiyya ya ce "Ahmad da É—alibansa su karhanta ta, su kuwa Abu Hanifa, Malik da Shafi'i ba su ma ji ta ba kwatakwata."
4- Da hadisin ya inganta, to riwayar ba zai a samu kokonto a wajen naƙalto ta ba. Da kai-tsaye kowa zai aminta da ita. Ta ma saɓa wa yanayin yadda tsarin salla yake. Riwayoyin ingantattu sun ci karo da ita." Majmu'u Fatawa Al'outhaymeen mujalladi na sha-huɗu babu salatuttaɗawwu'u.

Don haka idan mutum ya yi babu laifi, amma barin yin ta ya fi zama lafiya saboda rashin ingancinta.

Allah ne mafi sani.
Post a Comment (0)