LAYA SHIRKA CE, AMFANI DA ITA DON NEMAN WATA BUKATA BAYA HALATTA GA MUSULMI!



LAYA SHIRKA CE, AMFANI DA ITA DON NEMAN WATA BUKATA BAYA HALATTA GA MUSULMI!

 *TAMBAYA*❓ :

Assalaamu Alaikum warahmatullah...
Da fatan malam ya sha ruwa lafiya? Ubangiji ya karba mana ibadun mu!..

Malam shin akwai laya wanda ya halasta ayi amfani dashi? Misali, mutum yana tsananin rashin lafiya sai aka bashi magani ya dafa ya sha, amma cikin ruwan maganin akwai abu mai kamar laya, shin ya hukuncin wannan magani? Shin amfani dashi shirka ne, idan shirka ne wani iri?

Ubangiji ya saka da mafificin alkhayri!


 *AMSA*👇:

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillah wa ala alihi wa sahbihi ajma'in.

Laya mai sunan laya wacce muka sani, babu wata laya da ta halatta musulmi ya rataya ko yayi amfani da ita wajen neman jawo alkhairi gare shi, ko kuma kare kan shi daga wani sharri. Wannan ita ce maganar dake da hujja a shari'a. Laya ko ta alqur'ani ce, baya halatta musulmi yai amfani da ita don neman wata biyan bukata, wannan shine mafi ingancin zance da rinjaye, saboda hadisin Annabi sallallahu alaihi wa sallama inda yace

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: ((إِنَّ الرُّقَى وَالتَّمَائِمَ وَالتِّوَلَةَ شِرْكٌ)).

Annabi bai keɓance wani abu daga cikin ukun nan, sai ruƙya wacce babu shirka, amma sauran biyun ma'ana kowace irin laya (ta alqur'ani da wanin ta) da tiwala, shirka ne, abin da hadisin ke ishara ke nan. Duk wanda ya cire layar da aka yi da alqur'ani, yace ana iya amfani da ita, sai ya kawo hujja inda Annabi ya cire ta kamar yadda ya cire ruƙya shar'iyya kamar yadda yake a ƙasa 

عَنْ جَابِرٍ قَالَ نَهَى رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنِ الرُّقَى فَجَاءَ آلُ عَمْرِو بْنِ حَزْمٍ إِلَى رَسُولِ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالُوا يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنَّهُ كَانَتْ عِنْدَنَا رُقْيَةٌ نَرْقِي بِهَا مِنَ الْعَقْرَبِ وَإِنَّكَ نَهَيْتَ عَنِ الرُّقَى. قَالَ فَعَرَضُوهَا عَلَيْهِ. فَقَالَ: ((مَا أَرَى بَأْسًا مَنِ اسْتَطَاعَ مِنْكُمْ أَنْ يَنْفَعَ أَخَاهُ فَلْيَنْفَعْهُ)). 

عَنْ عَوْفِ بْنِ مَالِكٍ الأَشْجَعِيِّ قَالَ كُنَّا نَرْقِي فِي الْجَاهِلِيَّةِ فَقُلْنَا يَا رَسُولَ اللَّهِ كَيْفَ تَرَى فِي ذَلِكَ فَقَالَ: ((اعْرِضُوا عَلَيَّ رُقَاكُمْ لاَ بَأْسَ بِالرُّقَى مَا لَمْ يَكُنْ فِيهِ شِرْكٌ)). 

Don haka Mallama Fatima, idan har laya ce kamar yadda kika ambata, toh baya halatta a nemi waraka da ita. Hukuncin ta ya baiyana ƙarara cewa shirka ce, daga hadisin da muka koro a sama, don haka amfani da wannan magani bai halatta ba, Annabi yace, duk wanda ya rataya laya haƙiƙa yayi shirka, hadisin

6394 - «من علق تميمة فقد أشرك» .
(صحيح) [حم ك] عن عقبة بن عامر. الصحيحة 492.

Bayan haka a cikin lamarin amfani da laya, akwai ratayar da zuciya ga wannan laya da maras lafiya zai yi, Annabi sallallahu alaihi wa sallama yace duk wanda ya rataya wani abu, an dogarar da shi zuwa gare shi, ma'ana, addu'a ce, abin ya zamo abin dogaron sa ke nan, na'uzhu billah

دخَلتُ علَى عبدِ اللَّهِ بنِ حُكَيْمٍ وبِهِ حُمرةٌ، فقلت: ألا تعلِّقُ تَميمةً ؟ فقالَ:: نعوذُ باللَّهِ مِن ذلِكَ وفي روايةٍ الموتُ أقرَبُ من ذلِكَ، قالَ رسولُ اللَّهِ مَن علَّقَ شيئًا وُكِلَ إليهِ

Amma ya halatta ta cire layar ta sha maganin idan shi ma ba'a yi shi da najasa ko sinadari da Allah ya haramta.

Mallamai na kasa nau'ukan shirka gida uku ne, sune

1) *Shirkul Akbar* 
2) *Shirkul Asghar* 
3) *Shirkul Khafiyy* 

A nan mutum yayi Shirkul Akbar ne mai fitarwa daga musulunci. 

Sannan Mallamai suna rarrabe shirkul akbar zuwa gida huɗu, sune 

Shirku Adda'awah, Alƙasdi wanniyah, Almahabbah da shirku Aɗɗa'ah. 

Wallahu ta'aala a'lam.

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*
*_Gabatarwa_*

Yaku Yan'uwa masu Albarka ku taya mu yaɗa wannan karatu/sako zaku samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. 
     
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)