HAKKIN ANNABI (SAW) A KAN AL'UMMA
Bayan hakkin Allah babu hakki mafi girma a kan bayi kamar hakkin Annabi Muhammad (saw). Saboda shi ya fi soyuwa gare mu fiye da kawunanmu da iyayenmu da 'ya'yanmu. Kuma ya fi kowa cikin halitta tausayinmu da jin kai gare mu. Ba mu samu ilimi da shiriya da imani da kyawawan aiyuka da alheri da gyaruwan lamuran rayuwarmu ta Duniya ba sai ta hanyarsa (saw).
Shi ne wanda ya same mu batattu sai Allah ya shiryar da mu ta hanyarsa, ya same shaqiyyai tababbu sai Allah ya tsamar da mu ta hanyarsa, ya same mu cikin nau'ukan munanan aiyuka, na kafirci, fasikanci da sabo sai Allah ya dawo da mu kan imani da da'a da aiyukan alheri ta hanyarsa (saw).
Babu wani alheri face ya nuna mana shi, babu wani sharri face ya tsoratar da mu a kansa. Saboda haka yana da hakkoki masu yawa a kanmu, daga cikinsu:
1- Wajibi ne mu san cewa; shi Manzon Allah ne bisa hakika, kuma shi ne cikamakon Annabawa, babu wani Annabi a bayansa.
2- Mu san cewa; Allah ya aiko shi zuwa ga mutane gaba daya, Larabawa da Ajamawa, bakake da farare.
3- Mu san cewa; Allah ya aiko shi ne don ya yi bayanin Addini ga mutane, ya yi bayanin tushen Addini da rassansa, Aqidunsa da mas'alolin Fiqhunsa.
4- Mu san cewa; Allah ya aiko shi ne don ya gyara Aqidun mutane da aiyukansu da halaye da dabi'unsu. Ya zo ne don ya gyara Addini, kuma ya gyara Duniyar mutane.
5- Mu san cewa; shi ne mafi ilimi cikin mutane, mafi gaskiyansu, mafi yin Nasiha gare su. Ya fi kowa yin bayanin gaskiya, ya fi kowa sanin abin da zai gyara rayuwar mutane.
6- Wajibi ne mu yi imani da shi kamar yadda ya wajaba mu yi imani da Allah.
7- Wajibi ne mu yi masa da'a kamar yadda ya wajaba mu yi da'a ma Allah.
8- Wajibi ne mu so shi fiye da yadda muke son iyayenmu da 'ya'yanmu da kawunanmu da mutane gaba daya.
9- Mu bi shi a komai, kar mu gabatar da komai a kan Sunnarsa, kar mu gabatar da maganar kowa a kan maganarsa.
10- Mu girmama shi, mu daukaka shi, mu taimake shi, mu taimaki Addinin da ya zo da shi, mu taimaki Sunnarsa da dukiyoyinmu da harsunanmu da alkalumanmu da kawunanmu da dukkan abin da za mu iya.
11- Mu yi imani cewa; Allah ya tara masa dukkan falaloli da kamala ta Dan-Adam, abin da bai hadu ga wani mahluki ba. Shi ya fi kowa matsayi cikin halittun Allah, ya fi kowa daraja a cikinsu, kuma ya fi su girma da matsayi da falala da alfarma.
Annabi (saw) Yana da hakkoki masu yawa a kanmu, suna nan cikin littatafai.
#Zaurandalibanilimi
https://t.me/Zaurandalibanilimi