MENE NE ZAI TSERATAR DA BAWA DAGA WUTA?



MENE NE ZAI TSERATAR DA BAWA DAGA WUTA?

Abu Zarr Algifary RA yace: Nace Ya Manzon Allah (ï·º) mene ne zai tseratar da bawa game da wuta?

*Sai Yace: ((Yin Imani da Allah))*
Sai Nace: Ya Annabin Allah (ï·º) ai sai anyi aiki tare da Imanin?
*Sai Yace: ((Ya ciyar/kyauta komai ƙarancin abin da zai bayar daga cikin abin da Allah ya azurta shi da shi))*
Sai Nace: Ya Manzon Allah (ï·º) to, idan talaka ne fa ba shi da abin da zai bayar sadaka/kyauta?
*Sai Yace: ((Yayi umurni da abu mai kyau ya hana mummunan abu))*
Sai Nace: Ya Manzon Allah (ï·º) to idan ya kasance bashi da ilimi ba zai iya umurni da abu mai kyau ba balle ya hana mummuna?
*Sai Yace: ((Yayi aikata abin da zai amfane shi))*
Sai Nace: To idan shi din ba ya iya kyautata komai fa?
*Sai Yace: ((Ya taimaki wanda aka ci galaba/zalunta))*
Sai Nace: To idan ya kasance mai rauni ne ba zai iya taimakon wanda aka zalunta ba fa?
*Sai Yace: ((Kai ba ka son barwa wannan mutumin naka ko da alheri guda É—aya! To ya kula kada ya cutar da mutane))*
Sai Nace: Ya Manzon Allah (ï·º) idan ya aikata hakan zai shiga Aljannah?
*Sai Yace: ((Babu wani musulmi da zai aikata wani kyakkyawan aikin cikin waɗannan abubuwa face sai an riƙi har a shigar da shi cikin Aljannah))*

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)