Bayani Aka Rashin Biyayya Ga Mai Gida

*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*




Bayani Aka Rashin Biyayya Ga Mai Gida

Ki dubi sakamakon rashin yin biyayya: Kamar yadda kyautata wa maigida da girmamawa da darajtawa sakamakonsu yake gidan Aljannar ni’ima, haka nan munana zamantakewa ga maigida na iya jefa uwargida ga halaka ranar gobe kiyama. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya bayyana cewa mafi yawan ’yan wuta mata ne saboda rashin godiyarsu ga mazansu. A wani kaulin kuma ya ce da wata Sahabiya: “Ki kula sosai da yadda kika mu’amalance shi domin shi ne Aljannarki kuma shi ne wutarki.”

Haka nan duk matar da mijinta ya yi fushi da ita Wanda ke sama (Subhanahu Wa Ta’ala) Zai yi fushi da ita har sai mijin ya daina fushi da ita, kuma duk ibadunta ba a amsarsu har sai mijin ya daina fushi da ita.

Lallai akwai hadurra da yawa ga macen da take munana zamantakewa ga mijinta har mutuwa ta riske ta a wannan hali. Don haka uwargida sai ki auna ki gani, wanne ya fi miki muhimmanci; ki a je duk wani jiji-da-kanki da fadin rai, ki yi fatali da duk wani abu da ke kange ki daga yin ladabi da girmama maigidanki don ki tseratar da kanki daga azabar wutar Jahannama don ki dace da Aljannar Ni’ima. Lallai in kika duba sakamakon rashin girmama maigida, to duk wani abu da za ki yi don kubuta daga gare shi kadan ne, ga shi kuma girmama maigida na janyo alherai masu yawa tun a nan duniya mafi alfanu a cikinsu shi ne za ki samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan aurenki.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai su tura da cikeken sunansu tare daga in da take, ta wa'innan numba;* 👇 👇 👇

08162268959,08038902454
Post a Comment (0)