SHIRKA TANA CIKIN MANYA MANYAN ZUNUBAI MASU HALAKARWA!
Da sunan ALLAH Mai Rahama Mai Jin Qai.
Ya zo a cikin littafin sahihul Bukhariy da kuma na
Muslim daga Abu-hurairah (Allah ya kara masa yarda) daga Annabi (SAW) lallai shi ya ce:
*_"Ku nisanci abubuwa guda bakwai masu dulmuyarwa, Sai aka ce: Ya ma'aikin Allah, menene su? Sai ya ce: YIN SHIRKA WA ALLAH, DA SIHIRI, da kashe rai wacce Allah ya haramta kashe ta, face da haqqi, da cin dukiyar maraya, da karbar riba, da guduwa a ranar yaqi, da kuma yin qazafi wa kamammun mata, muminai, wadanda su ka gafala ga tunanin zina"_*
_{Bukhariy ne ya ruwaito shi, (lamba: 2766), da Muslim (lamba: 89).}_
📝Sai Annabi (SAW) ya bayyana mana a cikin wannan hadisin ingantacce cewa: Lallai shirka da sihiri suna cikin abubuwan nan guda bakwai masu halakarwa, kuma shirka ita ce mafi girmansu, saboda kasancewarta mafi girman zunubi, shi kuma sihiri yana daga cikin dangin shirka; wannan yasa Annabi (SAW) ya gwama ambatonsa da shirka; saboda su masu yin sihiri basa iya aiwatar da shi sai da yin bauta wa shaiɗanu, da kusantarsu da abubuwan da su ke so; kamar ta hanyar roqo (addu'a), shiyasa idan akaje neman addu'a a wajensu to aljanu suke roƙa ba Allah ba, ko yanka da bakance da neman taimako da makamantan haka.
Imam An-nasa'iy (Allah yayi masa rahma
) ya ruwaito daga Abu hurairah daga Annabi (SAW) lallai yace: *_"Duk wanda ya qulla wani qulli, sa'annan ya yi tofi a cikinsa to haqiqa ya yi sihiri, wanda kuma ya aikata sihiri to haqiqa ya aikata shirka, duk kuma wanda ya rataya wani abu to za a jivinta shi izuwa gare shi"_* {Nasa'iy a cikin (Sunan: 4079).}
Wannan kuma yana fassara faɗin Allah ta'alah a cikin "suratul falaq":
*_"Kuma ina neman tsarin Allah daga sharrin masu tofi a cikin qulle-qulle",_*
Maluman tafsiri su ka ce: (An-naffasaatu) su ne masu sihiri da su ke qulla qulle-qulle, sai su yi tofin kalmomi na shirka a cikinsu, suna masu kusantar sheɗanu da aikata haka don su zartar musu da muradansu na cutar da mutane da zaluntarsu.
Tabbas Shirka kafirci ne da zalunci babba, kuma ta hada da zuwa wajen wani malami rokonshi addu'a, ko kulla wani kulli, ko yace a yanka wata dabba don samun biyan buqata. Da makamantansu da yawa, wanda mata sun kware wajen neman taimako a wajen irin wannan mutanen. Kuji tsoron ALLAH, karku mutu akan shirka.
_Neman karin bayani, A duba/ Tafsirin Ibnu-jarir (24/704) wajen surar FALAQ, da tafsirin Ibnu-kasiir (8/526), da tafsirin Bagawiy (8/596)._
*✍️ Abdullah A Abdullah Abou Khadeejatu Assalafeey*
11/02/1443.
19/09/2021.
_*🎙ZAUREN SAWTUL HIKMAH 🎙 (da'awar sunnah a social Media's) 🌎*_
*• Ga masu buqatar shiga Zauren Sawtul hikmah zasu iya bi ta links din da ke ƙasa👇*
08032312988
https://t.me/sawtulhikma
https://www.facebook.com/sawtulhikmah
https://t.me/sawtul_hikmah
https://twitter.com/sawtulhikmah01
*🎙️SAWTUL HIKMAH TAKU CE DOMIN YAƊA SUNNA💪*