ANNABI DA SAHABBANSA //033



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*_وصلى الله على سيدنا ونبينا محمد وعلى آله وصحبه ومن سلك طريقهم إلى يوم الدين. صلوات الله عليه فى كل الأوقات عدد رماد الأرض أعدد المخلو قات_*

*❤️💞ANNABI DA SAHABBANSA //033❤️💞*

*(C) Baban-Manar Alqasim*

*MUTUM SHIDA DAGA YATHRIB*
Garin Manzon SAW da kowa ya sani da Madina ba sunansa na asali kenan ba, sunansa Yathrib, lokacin da Annabi SAW ya yi hijira zuwa can, sai ya zama babban birnin muslunci wato Madina, amma ya aka yi muslunci ya fara shiga can? A shekara ta 11 daidai lokacin aikin hajinsu, wanda ya dace da July 620 Miladiya lokacin ne aka sami wani digon muslunci da cikin lokaci qarami ya zama babban kogi har zuwa makadeden teku, da haka ya tabbata har abadin abadina.
.
Duk nau'o'in cutarwa da cin mutunci da azabtarwar da Annabi SAW yake fama da su, wani lokaci ma har da qoqarin kisa, duk wannan bai sa ya dena qoqarin kiransu ba don sauke wajibin da aka dora masa, koda kuwa babu masu shiga cikin addinin, sai dai a wannan karon yakan fita ne da daddare tsoron kar wani arne ya kawo cikas a tsakaninsu, an sami wani dare da Annabi SAW ya fita shi da Abubakar da Aliy RA suka bi ta gidajen Zahal da Shaiban bn Tha'alaba, ya kira su zuwa muslunci, har aka yi wata tauna-tauna mai ban sha'awa tsakanin Abubakar RA da wani dan qabilar Zahal, an yi wasu tambayoyi kuma qabilar Banu Shaiban sun ba da amsar da ta dace, sai dai wannan bai sa sun shiga muslunci ba.
.
Daganan sai Annabi SAW ya bi ta Aqabar dake Mina, nan ya ji muryar wasu mutane su 6 suna magana, duk 'yan Madina ne daga Khazraj:-
1) As'ad bn Zurara daga Banu Najjar.
2) Auf bnl Haris bn Rufa'a daga Banu Najjar.
3) Raafi' bn Malik bnl Ajlaan daga Banu Zuraiq.
4) Qutba bn Ámir bn Hadida daga Banu Salama.
5) Uqba bn Ámir bn Naabi daga Banu Haram bn Ka'al.
6) Jabir bn Abdillah bn Ra'ab Banu Ubaid bn Ganam.
.
Sa'ar da aka ci ita ce mutanen Yathrib wato Madina sun riqa jin Yahudawan dake zaune da su suna cewa "Annabimmu na wannan lokacin da za a aiko ya kusa zuwa, za mu bi shi mu hadu da shi mu yi muku kisar Adawa da Iramawa" kamar dai yadda 'yan Shi'a suke cewa Mahadi zai fito su hadu da shi su yi wa musulmai da Larabawa mummunar kisa, Annabi SAW na isa wurinsu ya tambaye su ko su waye, suka ce masa Khazrajawa ne.
.
Ganin haka sai Annabi SAW ya matsa kusa da su ya ce "Ku ne qawayen Yahudawa?" Suka amsa masa ya ce "Ko zan dan zauna mu yi magana?" Suka ce ba komai, suka zauna da shi ya yi musu cikakken bayani a kan muslunci, ya kira su zuwa ga tauhidi, ya karanta musu Qur'ani, daganan ne suka kalli juna suka ce "Wallahi wannan ne annabin da Yahudawa suke mana gargadi da shi, gaskiya mu riga su karbansa" nan take suka muslunta gaba daya, wadannan su ne manyan mutanensu wadan da yaqin cikin gida ya yi kaca-kaca da su, ga shi har zuwa lokacin bai qare ba, daga cikin abubuwan da suke kallo shi ne zai zama dalilin qarewar yaqin.
.
Suka ce "Mun bar mutanenmu a Yathrib ba wani abu a qirazansu sai gaba da juna da qiyayya, muna fata Allah SW ya sanya ka ka zama dalilin sake gamewarsu gaba daya, yanzu za mu koma mu kira su zuwa ga wannan addinin naka, in dai suka karba gaba daya, to ba wani mutumin da Allah zai daukaka a duniya kamarka" su kam kamar yadda suka yi wa Annabi SAW alkawari sun cika, domin suna isowa Yathrib suka ci gaba da yada da'awa, har sai da aka sami musulmi a kowani gida.
.
*AUREN ANNABI SAW DA A'ISHAH RA*
A watan Shawwal ne na wannan shekara ta 11 bayan samun annabci Annabi SAW ya auri A'ishah RA, tsakaninta da Sauda RA wata daya ne curcur, dukansu a watan Shawwal suka auri Annabi SAW, ita A'ishar ta auri Annabi ne tana 'yar shekara 6 kacal, kamar yadda galibin littafan tarihi suke cewa, kuma ya sadu da ita tana da shekara 9, wannan shekara ita ce daidai lokacin da mahaifar mace take gama saquwa ta shirya karbar jariri, sannan mace yanayin girmanta akwai 'yar shekara tara da za ka ganta a matsayin mace ce ta sosai a qirar jiki, don haka akwai buqatar mu san yadda A'ishah RA take a lokacin ba wai shekarunta ba.
.
*MAGANAR ISRA'I DA MI'IRAJI*
Akan sami sabani a lamuran fiqihu kuma a warware da ayoyin Qur'ani da hadisai, amma sau tari
Post a Comment (0)