YADDA AKE KARYA SIHIRI DA IZININ ALLAH




YADDA AKE KARYA SIHIRI DA IZININ ALLAH
********************************************
Idan kana tunanin anyi maka sihiri ko anyi ma wani 'Dan uwanka, Ko kuma matsalar Maita (Kambun Ido) to ga hanya mai sauki kuma halastacciya wacce Zauren Fiqhu ya dauko daga cikin irin fatawoyin da muke amsawa akan shafukanmu na Internet.
Da farko dai dole ka sanya hakuri da Tawakkali da tsoron Allah acikin zuciyarka. Ka fidda Qiyayya ko zargi atsakaninka da duk wani Musulmi. Sannan ka aikata wannan fa'idar :
1. Asamu ruwa cikin Bokiti, ka samo ganyen Magarya guda 7 ka dandakasu akan dutse da dutse sannan ka zuba acikin ruwan.
Ka tsoma babban yatsan hannunka na dama acikin ruwan. Ka kusanto da bakinka daf da ruwan. Sannan ka karanta wadannan ayoyi da surorin :
1. Fatiha.
2. Suratul Baqarah ayah ta 1-5. da kuma ayah ta 102-103. da kuma ayah ta 163-164. Da kuma ayah ta 255 - 257. Da kuma 285-286.
3. SURATU AALI 'IMRAAN : Ayah ta 18-19.
4. SURATUL A'ARAF : 54-56. da kuma 117-122.
5. SURATU YUNUS (AS) : Ayah ta 81-82.
6. SURATU TAAHA (AS) : Ayah ta 69.
7. SURATUL MU'UMINEEN : Ayah ta 115-118.
8. SURATUN NAMLI: Ayah ta 50-53.
9. SURATUL FURQAAN : Ayah ta 23.
10. SURATUS SAAFFAAT : Ayah ta 1-10.
11. SURATUL AHQAAF : Ayah ta 29-32.
12. SURATUR RAHMAN : Ayah ta 33-36.
13. SURATUL HASHRI: Ayah ta 21-24.
14. SURATUL JINN ayah ta 1-9.
15. SURATUL FEEL.
16. SURATUL IKHLAAS.
17. FALAQI da NAAS.
18. SURATU YASEEN.
Kana karantawa, Numfashin karatun yana sauka akan ruwan. Ba zaka cire hannunka ba, sai ka gama. Idan ka gama kayi salati ga Manzon Rahama (saww) kayi addu'a.
Sannan arika sha, kuma ana wanka dashi (wato shafawa ajiki baki daya). Har tsawon sati biyu. In sha Allahu kowanne irin sihiri ne, to Allah zai karyashi.
Hakanan za'a iya rubuta wadannan ayoyin da tawada mai tsarki sannan awanke da ruwan Zam zam ko ruwan sama, arika sha har ya Qare.
Sannan za'a iya karantawa acikin Man Zaitun ko Man Habbatus Sauda sannan arika shansa, ko kuma cinsa acikin abinci. Kuma ana shafawa.
Ana so Marar lafiyan ya yawaita Sadaqah da Istighfari da Salati ga Manzon Tsira (saww). Kuma ba'a so ahada wannan fa'idar tare da wasu Magunguna ko saiwa ko wani abu.
Idan duk an gwada wadannan amma ba'a samu cikakkiyar waraka ba, za'a iya kiran ZAUREN FIQHU ta wannan lambar domin samun shawarwari akan magungunan da za'ayi amfani dasu. 07064213990.
Allah yasa adace.
DAGA ZAUREN FIQHU (19/08/2017 27-11-1438).
IDAN KA SAMU DAMA KA BUGA KA RARRABA A MAKARANTU KO MASALLATAI DOMIN AMFANAR 'YAN UWA MUSULMAI. AMMA DON ALLAH KAR KA CHANZA KODA HARAFI GUDA.
Post a Comment (0)