💞DABI'UN MACE TA GARI💞



💞DABI'UN MACE TA GARI💞

💞Allah ya ce,

(فالصلحت)

 💞(Saboda haka, salihai) mata,

(قنتت)

💞(su ne Qanitat), wato masu biyayya ga mazansu, kamar yadda Ibnu `` Abbas da wasunsa suka fassara.

(حفظت للغيب) 

 💞(kuma wacce ta ke tsare kanta a lokacin da mijinta baya gida) As-Suddi da sauransu suka ce, wannan gaɓa tana nufin tana kare mutuncinta da dukiyar mijinta idan baya nan, da kuma fadin Allah,

(بما حفظ الله)

 💞(Da abin da Allah ya umurce su da su kiyaye.) Ma'ana, mai kariya (miji) shine wanda Allah ya kiyaye. Ibn Jarir ya rawaito cewa Abu Hurayrah ya ce Manzon Allah ya ce,

 *💞(Mafi alheri mace acikin mata, ita ce wacce idan ka kalle ta, za ta faranta maka rai, idan ka umarce ta sai ta yi maka biyayya, kuma idan ba ka nan, ta kiyaye mutuncinta da dukiyarka.)"* Sannan, sai Manzon Allah ya karanta fadin Allah, 

(الرجال قوامون على النساء).  

 💞(Maza sune mataimaka da kiyaye mata), har zuwa karshen ayar. Imamu Ahmad ya rawaito cewa `` Abdur-Rahman bin 'Awf ya ce Manzon Allah ya ce,

 *💞(Idan matar ta yi salloli biyar na farilla, ta azumci watan ramadan, ta kare farjinta kuma ta yi biyayya ga mijinta, za a ce mata, 'Shiga Aljanna ta duk kofor da kike so).'* 😍 

  💞Wacce kuwa bata bin umarnin mijinta, ta ke wasa da aurenta ko ohoo,🙄 sai dai ki ga matan kirki suna shiga. ALLAH ya tsareku ya baku ikon yiwa mazajenku biyayya da soyayya. 🌺


*✍️Abou Khadeejatu Assalafeey🕊️*
18/09/1442.
31/05/2021.

SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss
Post a Comment (0)