ANNABI DA SAHABBANSA // 083


ANNABI DA SAHABBANSA // 83
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
Jiya-jiyan nan aka gama yaqin Uhud, ko doguwar tafiya mutum ya yi wani lokaci yana buqatar hutu a qalla na kwana 2 zuwa 3, bare kuma ba-ta-kashi aka yi da kafurai, masamman da yake wannan yaqin ba kamar na Badar ba ne, an mutu gaskiya, ko ginan qabarin mamatan kawai zai gajiyar, amma duk da haka sahabbai suka sake daura damara suka amsa kiran Annabi SAW don daukaka addini.
.
To da yake Annabi SAW ya sanya dokar cewa wanda ba a yi Uhud da shi ba kar ya bi su, kenan neman da Abdullah bn Ubay ya yi na hawa abin hawa da Annabi SAW ba zai sami karbuwa ba sam, Jabir bn Abdillah ya ce "Manzon Allah, zan so a ce duk inda za ka tafi qafata-qafarka, to sai dai mahaifina Abdullah ya bar min nauyin kula da qannina mata, ka ba ni damar fita tare da kai" Annabi SAW ya yi masa izini, haka suka yi tafiya tare da Annabi SAW na tsawon mil 36 daga Madina, suka kafa sansani a can.
.
Tunanin da Annabi SAW ya yi na yuwuwar kwanowar mushrikai ya zama gaskiya, domin lokacin da suka isa Rauhaa kimanin mil 36 daga Madina suka fara zargin juna kan yadda yaqin ya qare, don ya bayyana qarara cewa su suke da nasara, suka ce wa junansu "Kun yi wa musulmai mummunar illa, sai kuma ku bar su lafiya lau ga gwarazansu da rai yadda za su yi muku wani sabon shiri? Gaskiya a koma a gama da su gaba daya"
.
Bisa ga dukkan alamu mai ba da wannan shawarar ya dubi qarfin mushrikan ne kawai bai duba na musulman ba, don inda a ce musulman kanwar lasa ne da tun karon farko an gama da su, wannan ya sa kwamandansu Safwan bn Umayya ya bijire wa lamarin ya ce "Jama'a ku sake shawara, ina muku tsoron kar wadan da tun farko ba su fito ba a zo wannan karon su hadu da wadan da muka gwabza da su su qara qarfin yi mana illa"
.
In kun tuna dama mun karanta a baya cewa fitowar da muminai suka yi musu ta bayan gida sun yi tsammanin qofar raguwa aka yi musu, dole wasu suna cikin Madina, don ba yadda za a yi musulmai su fito gaba daya su bar musu tsahhi da qananan yara, don haka Safwan ya ce "Ku mu koma, ban da sakankancewar in muka koma Madina wannan karon mu ke da nasara" duk da kasancewarsa babba maganarsa kuma abar ji ce wannan karon ba ta sami karbuwa ba ko kadan, nan take rundunar ta yi kwana zuwa Madina a karo na 2.
.
A baya an ce Ma'abad bn Abi-Ma'abadil Khuza'iy ya zo wurin Annabi SAW ya muslunta, (Ko da yake wasu sun ce bai muslunta ba yana dai ba wa Annabi SAW shawara ne sabo da qawancen da ke tsakanin Khuza'a da Banu Hashim) yake ce wa Annabi SAW abin da ya sami sahabbanka ya yi matuqar damunmu, muna fata Allah ya kare ka" lokacin ne Annabi SAW ya sa shi ya dama wa Abu-Sufyan lissafi, to kafin Abu-Sufyan din ya kwano da rundunarsa zuwa Madina Ma'abad din ya same shi.
.
Da ma Abu-Sufyan bai san da musluncinsa ba, don haka da ganinsa ya tambaye shi "Ma'abad me ke faruwa ne?" Nan fa ya kai masa farmakin ruwan sanyi ya ce "Na ga Muhammad ya fito tare da mutanensa cikin gayyar da ban taba ganin irinta ba, ba shakka rundunarsa da wadan da tun farko ba su fito Uhud ba sun shirya muku, sai ma nadamar rashin fitowarsu suke yi, gaskiya suna cikin matsanancin son su gama da ku"
.
Abu-Sufyan ya ce "Kai ar! Me kake nufi ne?" Ya ce "Manufata kar ka motsa daga nan har sai ka ga rundunarsu ta farko da za su fito ta bayan wadancan tsaunukan" Abu-Sufyan ya ce "Ai wallahi mun yi shirin gamawa da su kaf" ya ce "Ina ba da shawarar kar ai haka" daga nan gabansu ya fadi, tsoro ya shiga cikin zuciyarsu har yake ganin mafita kawai a koma Makka.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)