ANNABI DA SAHABBANSA // 084


ANNABI DA SAHABBANSA // 84
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
Duk da karayar zuciyar da aka samu sai da Abu-Sufyan RA shi ma ya yi qoqarin musayar farfagandar yaqi kan musulmai don ya hana su qarisowa wurinsu, kusan ya ci nasarar yin hakan, babban abin da yake tsoro a ce an yi musu korar kare, in da za su koma Makka a haka za su iya cewa su ne suka ci nasara kuma sun jigata musulmai ko da kuwa ba fursunonin yaqi ba ganima, sai ya ga wani ayari na Abdul-Qais wanda zai nufi Madina ya ce musu "Ina da saqon da nake so ku isar min ga Muhammad, in kuka dawo Makka na shaqe muku dabbobinku da zabibi?"
.
Suka amsa, ya ce "To in kuka hadu da shi ku gaya masa cewa mun juyo da rundunarmu muna son mu gama da shi, shi da sahabbansa gaba daya" ayarin suka sami Annabi SAW da sahabbansa a Hamra'ul Asad suka gaya masa abin da Abu-Sufyan ya aiko su da shi, suka ce "Mutanenku fa sun yi muku taron dangi, ku ji tsoron gamuwa da su" a maimakon su tsorata sai maganar ta qara musu qwarin gwiwa.
.
Haka dai Annabi SAW ya tsaya a nan Hamra'ul Asad din bai yi gaba ba bai baya ba, tun daga yammacin Lahadi, Litini, Talata a Laraba 11 ga watan Shawal shekara ta 3 (11/09/0003) Annabi SAW ya kamo hanyarsa ta komawa Madina, to dama mun yi maganar Abu-Izzatul Jamhiy mawaqin da aka kama a Badar ya yi alqawarin ba zai sake sanya baki a yaqi Annabi SAW ba, aka tausaya masa aka sake shi sabo da tarin 'ya'ya matan da ke gabansa.
.
Ai kuwa yana komawa Makka kwadayi ya sa ya canja shawara ya saba alkawarinsa da Annabi SAW, kwatsam sai aka sake yin carab da shi a Uhud, ya ce "Muhammad a sanya min fansa, a taimaka min, a bar ni ga yarana mata, na yi maka alqawarin ba zan sake wannan aika-aikar ba" sai dai maganarsa ba ta sami karbuwa ba.
.
Annabi SAW ya ce "Ai ta qare, ba za ka sake komawa Makka ka ce wa jama'arka na yaudari Muhammad sau biyu ba, tun karon farko mai hankali ke daukar darasi" Ya sanya Zubair ne ko Aasim bn Thaabit ya fille masa kai, ya kuma yanke wa dan leqen asirin Quraishawa hukuncin kisa.
.
Wato Mu'awiyya bnl Mugeera bn Abil-Aas, kakan Abdulmalik bn Marwan ta wurin uwarsa, abin da ya faru kuwa ya bi ta wurin dan baffansa ne wato Usman bn Affan ya nemi kariya, Usman RA ya nema masa kariya wurin Annabi SAW aka ba shi bisa sharadin in aka same shi bayan kwana 3 a kashe shi, da musulmai suka bar Madina sai ya yi zamansa, ya riqa tara bayanan sirri don ya kai wa Quraishawa.
.
Annabi SAW na dawowa da rundunarsa sai Mu'awiyya bnl Mugeera ya yi qoqarin ficewa ya arce, Annabi SAW ya sa Zaid bn Haaritha da Ammaar bn Yaasir su bi shi, suka kuwa kama shi suka gama da shi, kenan in an tattara za a iya cewa yaqin Hamra'ul Asad ba wani yaqi ne mai zaman kansa ba yaqin Uhud ne, wannan a taqaice nan ne yaqin Uhud ya qare gaba dayansa, bisa ga al'ada duk wanda ya zo wuri ya ci shi da yaqi yakan tsaya na kwana 3 don tabbatar da rinjaye kafin ya wuce, Quraishawa kam a ranar asabar din suka bar Uhud, in ma mun dauki Hamra'ul Asad ne suna can Rauhaa ba su ko iya kwanowa ba.
.
Musulmai kuma bayan sun koma cikin garinsu wato Madina sun sake fitowa don raka Quraishawa, kuma sun tsaya a Hamra'ul Asad din har kwana 3, in aka dauki Quraishawa a matsayin mahara sai a ga sun kasa mamaye wuri, ba ganima ba fursununin yaqi, musulmai kuwa da aka fado musu sun jajurce har qarshen yaqi, sun hana shiga garinsu, ba a kama ko dayansu ba, ba a ci ganimansu ba, sun yi nasara, da sun tsere kamar yadda ake cewa da ba haka ba. 

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)