ANNABI DA SAHABBANSA // 85
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
YAQOQIN DA ANNABI YA TURA KAFIN AHZAAB
Sau da yawa in aka nemi cin galabarku a wajen yaqi wasu kan ga dama-damarku, abin da ya faru da musulmai kenan a Uhud, ba Quraishawa ko Larabawa ba har yahudawa da munafuqai sun fara qoqarin fito musu, dama Badar ce ta fitar da jarumtarsu a fili, yanzu mushrikai sun fara ganin dama ta samu da za su ci karensu ba babbaka, wata 2 kacal da yin Uhud har Banu Asad sun shirya wani mummunan hari da za su kai Madina.
.
Qabilar Adl da Qaara kuma suka shirya wata maqarqashiya a watan Safar shekara ta 4 wace ta yi sanadiyar salwantar da rayukan sahabbai 10, a watan dai Banu Aamir su ma suka dabbara wata manakisar da ta kai ga mutuwar sahabbai 70, har ake kirar hargitsin da hargitsin Bi'iru Ma'uuna, a Rabi'ul Auwal shekara ta 4 Hijiriyya Yahudawan Banu Nadeer suka yi yunqurin kashe Annabi SAW, Banu Gatafaan ma suka yi yunqurin kai wa Madina farmaki.
.
Da yake an dan sha wahala a Uhud Annabi SAW bai yi yunqurin fita da sojojinsa nan da nan ba, ya dan bar su don su sarara, qarfinsu ya dawo, har su da kansu su fara jin cewa abin da ake yi musu fa ya isa dole a fito a kare muslunci da martabarsa, a qarshe abin da ya faru kenan, nan take babban kwamandansu, jagoransu kuma Annabinsu, SAW ya fara shirya wasu hare-hare da za a kai wurare daban-daban don maido da martabar musluncin.
.
HARIN ABU SALAMA
Da ma wadanda suka fara yunqurin kai wa musulmai hari bayan gwagwarmayar Uhud Banu Asad bn Khuzaima ne, 'yan leqen asirin muslunci sun dauko labarin cewa Talha da Salama 'ya'yan Khuwailid sun je wa qabilarsu da masu dangantaka da su suna tunzuro su kan kawo wa Annabi SAW hari, Annabi SAW ya riga su yunquri, inda ya tura musu sojoji 150 ciki Muhajirai ne da Ansarawa.
.
Sun fita ne qarqashin jagorancin Abu-salama RA, in da ya auka musu kafin su farga, dole haka suka watse, musulmai suka kwashe guzurinsu na raquma da sauran bisashe a matsayin ganima, suka kado su suka dawo Madina cikin izza, ba tare da wani yaqi ba, sun fita a farkon kamawar watan Muharram ne shekara ta 4, da ma can Abu-Salama yana da rauni a yaqin Uhud da ya gabata, dawowarsa wannan harin ba jimawa ya ce "Ga garinku nan".
.
HARIN ABDULLAH BN UNAIS
A rana ta 5, na wannan watan, wato Muharram shekara ta 4, 'yan leqen asirin muslunci suka kawo labarin cewa Khalid bn Sufyanil Huzaliy yana tara jama'a don ya yaqi muslunci, nan take Annabi SAW ya tura masa Abdullah bn Unais Alhuzaliy don ya gama da shi, Abdullah ya bar Madina na tsawon kwana 18 sannan ya dawo ranar Asabar da kan Khalid ya gama da shi, shi ne Annabi SAW ya ba shi sandar girma wace da mutuwarsa ta zo ya nemi a burne shi da ita (Zaadul Mi'aad 2/109, Ibn Hisham 2/619-620)
.
HARIN RAJEE
A watan Safar ne na wannan shekarar wato shekara ta 4 Hijiriyya wasu daga cikin qabilar Adl da Qaara suka ce sun muslunta amma suna buqatar wadanda za su karantar da su Qur'ani, sai Annabi SAW ya tura musu mutum 10 (kamar yadda Buhari ya rawaito), ya shugabantar da Marthad bn Abi-Marthad Alganawiy, Bukhari ya ce Aasim bn Thaabit ne wato kakan Aasim bn Umar bnl Khattab, suna isa Rajee, wani makwancin ruwa na Huzail tsakanin Raabag da Judda sai suka qwalla ihu.
.
Nan fa wasu qauyuka na Banu Lahyaan suka fito suka bi sawunsu a hankali har suka yi musu qawanya sannan suka ce musu "Mun yi muku alkawarin cewa matuqar kun sauka a inda muke ba za mu yi muku komai ba" Aasim ya qi yarda ya far musu shi da jama'arsa har sai da aka kashe mutum 7 da kibau, sai Khubaib da Zaid bn Dathna da dayan na ukun suka rage, su ma suka sake yi musu wani alkawarin na barinsu in sun sauka.
.
Sai na ukun ya ce "Wannan wata sabuwar yaudarar ce" suka dauko shi suka yi masa magani kan ya bi su, da yaqi suka kashe shi, Khubaib da Zaid kuma suka tafi da su Makka suka sayar, kar a manta sun kashe iyayensu a Badar, don haka suka jefa Khubaib a kurkuku daga bisani suka dauke shi da Haram zuwa Tan'eem don su tsire shi.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248