ANNABI DA SAHABBANSA // 086

ANNABI DA SAHABBANSA // 86
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
QURAISHAWA SUN TSIRE KHUBAIB
In mun tuna daya daga cikin dalilan da za su iya sanya sojojin muslunci su qi yarda su shiga hannun Quraishawa har da rashin sanin abin da zai iya biyowa bayan kama su, tabbas Khubaib kusan abin da ya faru da shi kenan, Quraishawa ba su saye shi don ya yi musu hidima kamar yadda sauran bayi suke yi ba, don kuwa sun kawo shi Tan'eem ne kamar yadda muka karanta, suka taru a can suka yi qoqarin tsire shi, nan ne ya nemi su bar shi ya yi nafila raka'a biyu, da yake sun san ko me zai yi dai kashe shi za su yi sai suka bar shi.
.
Khubaib RA ya yi nafilarsa a qarshe ya ce "Wallahi ba don tsoron kar ku ce mutuwa nake gudu ba da na qara" daga nan ya yi addu'o'i a kansu" wani fitaccen mutum ya ce "Ranka zai maka dadi a ce Muhammad na gabanmu muna qoqarin fille masa kai, kai kuma a ce kana cikin iyalinka?" Ya ce "Wallahi ina! Sam ba zan so a ce ina cikin iyalina kuma Annabi SAW yana inda yake mummunan abu ya same shi ba!"
.
A qarshe dai haka suka tsire shi, suka sa wani ya yi gadin gawar, har sai da Amr bn Umayya Addamriy ya wayance ya tafi da gawar cikin dare ya rufe ta, wanda aka ba wa alhakin kashe shi shi ne Uqba bnl Haarith, Khubaib ne ya kashe ubansa a Badar, da wannan za mu ce Khubaib ne mutumin farko da ya fara neman a bar shi ya yi nafila kafin a kashe shi.
.
Shi kuwa sahabin na biyu wato Zaid bnd Dathna Safwan bn Umayya ne ya kashe shi a maimakon mahaifinsa da aka kashe, ko irin wannan mu'amalar kawai ta isa ta sa musulmai su kauce wa shiga hannun mushrikai ta kowani hali, don sun kama mushrikan a Badar kusan mutum 70, amma ba su kashe su don abin da suka yi musu kafin hijira ba.
.
Bayan nan Quraishawa suka tura wasu su yanko musu wani abu na jikin Aasim don su gani ko shi ne, don ya kashe wani babbansu a Badar, Allah SW ya tsare gawarsa suka kasa yin komai da ita, dama Aasim ya roqi Allah da ya kare gawarsa daga mushrikai, da labarin ya iske Umar RA ya ce "Allah kan kare bawansa mumini da ransa ko bayan mutuwarsa" (Buhariy 2/568, Zadul Mi'ad 2/109)
.
ABIN TAKAICIN DA YA FARU A BI'IRI MA'UNA
Bayan wannan abin takaicin da ya faru a bakin ruwan Rajee' wanda ya fi shi muni ya kuma faruwa, abin da ya faru shi ne Abu-Barraa wato Aamir bn Maalik ya zo wurin Annabi SAW, sai Annabin ya kwadaitar da shi muslunci, duk da dai bai muslunta ba amma bai nuna qin haka din ba, sai ya ce "Manzon Allah, da za ka tura mutanenka su je Najad su yi da'awa a can da zai fi, wata qila mutanen su muslunta".
.
In ba mu manta ba Annabi SAW ya taba tafiya can ya san yadda ta kaya, sai ya ce "Ina jin mutanen Najad din nan" Abu Barraa ya ce "Kar ka ji komai zan tsaya musu" sai Annabi SAW ya zabo mutum 70 ya dora Munzir bn Amr daya daga cikin Banu Saa'ida, ba shakka, manya ne kuma zababbu, masana Qur'ani, sukan yi itace ne don samun abin da za su saka a bakin salati, in suka dawo da daddare kuma su shiga karatun Qur'ani, suna cikin ahlul Suffa ne, haka dai suka fita kamar yadda aka nema.
.
Ruwan Ma'una wani wuri ne da ke tsakanin Banu Aamir da Banu Sulaim, sahabban nan na isa suka sauka a can, suka aiki Haraam bn Malhaan dan uwan Ummu-Sulaim da takardar Annabi SAW zuwa ga abokin gaban Allah wato Aamir bnl Tufail, ko kallonta bai yi ba ya sa wani da ke bayansa ya caka masa mashi, yana caka masa jini ya fito Haraam ya ce "Allahu Akbar, na rantse da Ubangijin Qa'aba na rabauta".

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248

Post a Comment (0)