ANNABI DA SAHABBANSA // 087
.
.
Aamir bnl Tufail na kashe Haraam ya yi maza ya je wajen Banu Aamir ya tunzuro su don su zo su yaqi sauran sahabban, sai aka yi dace suka qi amsawa, amma qabilar Asiyya, Ra'al da Zakwaan suka amince kuma suka fito suka mamaye sahabban Annabi SAW aka gwabza, amma qarfin ba daya ba don haka suka gama da sahabban gaba daya sai dai Ka'ab bn Zaid bnn Najjaar shi ne ya yi saura zuwa yaqin Khandaq inda aka kashe a can.
.
Amr bn Umayyad Damriy da Munzir bn Uqba bn Aamir suna cikin musulman da aka turo, suna can suka hango tsuntsaye suna zazzaga inda abin ya faru, Munzir ya zo ya fafata da su har shi ma suka kai shi lahira, suka kama Amr bn Umayya, da suka ji cewa daga Mudar yake sai Aamir ya jawo gashin kansa ya 'yanta shi don abin da ke kan mahaifiyarsa na 'yantarwar, shi kuma Amr ya koma wa Annabi SAW da duk abubuwan da suka faru, ba shakka wannan ya ma fi Uhud tsanani.
.
Koda yake a Uhud ma mutum 70 aka kashe kamar wannan, sai dai wannan zababbu ne, kuma kisar ba a yaqi ta auku ba, don da yaqi ne yakan fi dama-dama an san wannan akwai yuwuwar faruwar nasara ko asara, wata rana Amr na tafiya a hanya ya zo qarqashin inuwar wata bishiya ya sauka.
.
Can sai wasu mutane su 2 daga Banu Kilaab suka sauka tare da shi, ya bari har sai da suka yi barci ya gama da su, ya yi haka ne don daukar fansar abin da suka yi wa mutanensa kwanan nan, ashe suna da alkawari da Annabi SAW bai sani ba, yana zuwa ya labarta wa Annabi SAW abin da ya faru, ya ce masa "Don me ka kashe su" da yake Annabi SAW ya san dalili sai ya fara tattara diyyarsu ga mutane, cikin wadanda aka nema a hannunsu har da Yahudawa.
.
Yahudawa sun shugo ciki ne don dama wannan yana cikin alkawarin da aka yi da su, a iya cewa dalilin da ya jawo yaqin Banu Nadeer kenan ( Ibn Hisham 2/183, Zadul Mi'ad 2/109, Buhari 2/586), za mu duba hakan in lokacinsa ya zo, wadannan ababan takaici guda 2 tabbas sun tabi Annabi SAW, amma da yake muslunci ba yaqi ne a gabansa ba da'awa ce don shugo da al'umma cikin tsira sai Annabi SAW ya fara yin qunuti a salla.
.
Wannan yana dada tabbatar da cewa muslunci bai yadu da bakin takobi ba, duk yaqoqin da muka ambato a baya za mu ga kodai mushrikan sun taso sun zo gamawa da musulmai sai Annabi SAW da jama'arsa su fito su kare kansu, ko kuma a sami labarin shirin sa suke yi a bi su a wargaza su kafin su dauki matakin da zai yi wa muslunci lahani.
.
In har akwai wani dalili wanda zai sa musulmai su yaqi kafurai to bai kai wadannan aika-aikan guda biyu ba, duk da haka ba a yaqe su ba sai qunuti Annabi SAW ya riqa yi, shi ma din bai yi nisa ba ya bari da umurnin Allah SW, don haka masu yin qunuti don Allah a kiyaye, ban da addu'ar girgizar qasa da manyan masifu, don in suka zo ba kafiri kadai za su shafa ba har da musulmi, Allah SW ya ce ku ji tsoron fitinar da ba musulmi kadai za ta shafa ba.
.
YAQIN BANU NADEER
Yadda muka karanta a baya mun tarar da cewa Yahudawa suna da mummunar adawa da musulmai kuma za su yi matuqar jin dadi in mummunan abu zai sami musulman, sai dai duk da haka ba sa yarda a yi fito na fito da su, sai dai su gwara mutane su yi ta kashe junansu saboda su sami wani abin da suke so ko da kuwa bai da yawa, a qarshe dai su ba su yi asarar komai ba, duk kuwa da alqawarin da ke tsakaninsu da musulmai wanda suka rattaba hannu a kai, ko da yake abin da ya faru da Banu Qainuqa da Ka'ab bnl Ashraf ya dan razana su kadan har sun dan natsu kamar sun kintsu.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248