ANNABI DA SAHABBANSA // 090
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
YAQIN BADAR NA BIYU
Bayan musulmai sun gama da abokan gaba na gida da na kan hanya sai kuma hankulansu suka koma kan mushrikan Makka wadanda aka yi alqawarin haduwa da su bana a qarshen yaqin Uhud, a watan Sha'aban ne shekara ta 4 Hijiriyya wanda ya zo daidai da January 626 Miladiya Annabi SAW ya fita cikin sahabbansa 1500 don fuskantar abokan gaba, rundunar tana da dawaki 10, kwamandan yaqin kuma shi ne Aliy RA, sai Annabi SAW ya dora Abdullah bn Rawaha a matsayin mai kula da gari, ya riga kafurai zuwa Badar, ya sauka a can yana jiransu.
.
Kwamandansu a lokacin wato Abu-Sufyan RA, ya fito ne cikin sojojinsa 2,000, da dawaki 50, dawakin za mu iya kwatantasu da machine-gun a yau, don haka duk yaqi sai ka ji an ambato yawansu, kafurai suna da 50, musulmai suna da 10, yawan kafurai 2,000 na musulmai 1,500, duk da cewa kusan kankankan ake, amma in aka duba kayan yaqin sai a ga har yanzu akwai tazara a tsakankanin bangarorin guda biyu, rundunar kafurai dai ta iso Majanna, wani ruwa ne da ke kwance a can, a nan ne ma suka sauka gaba daya.
.
Kwamandan nasu ya riga ya sha jinin jikinsa, don ba wannan ne karon farko da suka fara gwabzawa ba, ko da yake sun yi wa musulmai barna a yaqin Uhud, sai dai duk sun san yadda yaqin ya qare, tabbas tsoro ya dan shige shi, suna qarisawa Zahraan sai ya fara saqa yadda zai wayence ya koma gida, nan ya ce wa jama'arsa "Quraishawa, ina tabbatar muku da cewa wannan shekarar ba ta dace da kuyi yaqi a ciki ba"
.
Ya ce "Shekarar da ta dace ita ce wace akwai yabanyar da dabbobinku za su yi kiwo har ku sami isasshen nono, don haka ina umurtarku da ku koma gida, ni kun ga komawata" bisa ga dukkan alamu ko su sojojin kowa jininsa a qumba yake, don ba wanda ya yi jayayya bare ya turje kan cewa lallai sai an je fagen fama nan kamar yadda aka yi alqawari, ba su ma ambato alqawarin da suka yi ba bare su yi tunanin za a ce sun ji tsoro, bare kuma su ambato daukar fansa ko gamawa da musulmai gaba daya.
.
Haka dai musulmai suka zauna a Badar har tsawon kwana 8 ba ko alamar Quraishawa, suka qaraci jiransu suka dauko hanyar Madina, duk Larabawan da ke bibiyar adawar sun san wa yake da rinjaye kuma shi ya kamata a ji tsoronsa, Annabi SAW ya koma Madina lafiya lau, yanzu in sahabban Annabi SAW sun kafurce masa ne bayan rasuwarsa ya sa Shi'a suke tsine musu, to ina daruruwan da suka yi shahada kafin rasuwarsa? Zancen banza ne kawai, musluncin suke qoqarin batawa, ba kuma zai baci ba sai tare da bata sahabban da suka yada shi.
.
HARIN DAUMATUL JANDAL
Sai dai bayan wata 6 kacal daga dawowa yaqin Badar na biyu, 'yan leqen asirin Annabi SAW suka kawo labarin cewa qabilolin da ke can Daumatul Jandal da ke bangaren Sham suna tsare hanya suna qwace don tara abin da za su yaqi Annabi SAW da shi a Madina, sai Annabin ya dora Sibaa' bn Urfuta Algifari a matsayin mai kula da gari, mu lura da wadanda Annabi SAW ke ba wa tsaron gari, in yana nufin iyalin gidansa ne za su gaje shi, tabbas zai kebance su da wannan aiki, don ko a Makka din cikin rundunar Quraishawa kowace qabila da muqamin da take riqewa wata ba ta shiga na wata.
.
Kenan Annabi SAW bai kebe wasu banda wasu ba, wanda ba a yarda da shi ba ba a ba shi tsaron gari, ko lokacin ba ahlul baiti ne sai sahabban? In ba su kenan sahabban ne suka yi yaqi don yada addinin Allah da taimakon manzonsa ba su ba, asali Annabi SAW bai bambance wasu ahlul baiti da sahabbai ba wajen fita yaqi ko da'awa, musulman qwarai ma bayansa ba su yi haka ba, sai dai masu qoqarin bata sahabban a yau.
.
Annabi SAW ya fita cikin sahabbai 1,000 a watan Rabi'ul Auwal na shekara ta 5 Hijiriyya, ya dauki wani daga cikin Banu Azrah wato Mazkuur don ya nuna musu hanya, ya riqa tafiyar ne cikin dare yana buya da rana don ya fado wa kafuran ba tare da sun sani ba, aka kuwa yi sa'a hakan ta faru, suka fashe kowa ya miqi hanyarsa suka bar bisashensu suka tsere, wasu sun tsira wasu kuma an illata su, lokacin da suka qarisa Dumatul Jandal ba su iske kowa ba duk sun watse, Annabi SAW ya tsaya can na 'yan kwanaki.
.
A nan ne ya riqa tura sojoji wurare daban-daban, sai dai ba wanda aka samu, daga bisani ya dawo gida shi da sojojinsa, yanzu ba cikin Madina ba hatta kewayenta ba inda ake jin tsoron wani, zai yi kyau a fahimci cewa duk inda suke qarqashin musulman nan fa ba inda aka sanya su su shiga muslunci a dole, in dai sun shirya za su yaqi musulmai ne sai a je a wargaza su kafin ma su iso Madina, wanda ya muslunta wannan kuma shiriya ce ta Allah SW, sanyin da Quraishawa suka yi ya ba musulmai damar da'awa.
Rubutawa:- Babban Manar Alqasim
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura
Daga
*MIFTAHUL ILMI*
ZaKu iya Bibiyar Mu a
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248