ANNABI DA SAHABBANSA // 089


ANNABI DA SAHABBANSA // 89
.
Mawallafi: Baban Manar Alqasim
.
Ba Abdullah bn Ubay ba ko Yahudawan Banu Quraiza ba su iya tabukawa da komai ba, ba wanda ya iya kai dauki, shi ya sa Allah SW ya kwatanta su a suratul Hashr da shedan, wanda zai sa mutum ya kafurta a qarshe ya ce ba ruwansa shi yana tsoron Allah, haka suka bar Banu Nadeer cikin mamaya na kwana 6, wasu suka ce kwana 15 ne, sai Allah SW ya tura musu tsoro, suka yar da makaman da kuma miqa wuya, don haka suka tura wa Annabi SAW da saqon cewa "To mun yarda za mu bar Madina"
.
Jin haka sai Annabi SAW ya ba su sharadin cewa suna da damar fita da iyalansu gaba daya, da ma duk abin da raqumansu za su iya dauka sai dai makamai, su kuma don kar su bari musulmai su amfana da su sai suka fara rusa gidajensu da hannayensu, duk suka kwashe qofofi da hunduna, wasu har itatuwan rufi sai da suka tarkata, suka kwaso matansu da qananan yaransu suka dora a kan raquma 600, suka kama hanyar Khaibar, har da shugabanninsu kamar shi Huyay bn Akhtab din da Salaam bn Abil-Haqeeq, wasu kuma suka nufi Sham wato Palestine kenan.
.
Ko da yake an sami mutum biyu da suka muslunta a cikinsu: Yameen bn Amr da Abu-Sa'ad bn Wahab, su kam ba a taba musu komai ba, sauran makaman da suka shiga hannun musulmai na Banu Nadeer sun hada da sulke 50, takubba 350 da sauransu, sai kuma aka mamaye qasar da suka bari da gidajensu da duk abin da ya yi saura, yanzu komai ya dawo hannun Annabi SAW a matsayin shugaba kuma jagora, shi ne zai sanya su a inda ya dace.
.
An yi wannan yaqi na Banu Nadeer ne a watan Rabee'ul Auwal shekara ta 4 Hijiriyya, wanda ya yi daidai da August 635 Miladiya, inda Allah SW ya saukar da suratul Hashr kacokan dinta ta yi bayanin yadda komai ya wakana na korar Yahudawa, da tona asirin munafukai, da yadda ake raba fai'i tunda ba yaqi aka fafata ba.
.
A ciki ne ya yaba wa Muhajirai da Ansarawan da Shi'a ke zaginsu, sare bishiyoyin dabino da qona su kuma Allah SW ya ce da izininsa ne aka yi, ba fasadi aka yi ba, ya umurci muminai da su riqe taqawa, su kuma yi shiri don lahirarsu, a qarshe ya qarqare da yabon kansa ta ambato sunayensa tsarkaka, in muka dubi irin tsiyar da Yahudawan nan suka tsula a Madina da karya dokokin da suka yi, da ma qoqarin kashe Manzon Allah SAW, jagoran muslunci sannan suka fara harbo musulmai da kibau sai mu ga adalcin muslunci da aka ce su koma inda suka baro kawai ba tare da ko qwarzane ba.
.
YAQIN NAJAD
Wannan nasara ta fatattakar Yahudawa daga tsakankanin musulmai ta ba wa Annabi SAW da sauran sahabbai RA qwarin gwiwar fuskantar abokan gaban da ke waje, wadannan kafuran sun kashe gwaraza kuma masana Qur'ani kamar yadda muka fadi a baya, har abin ya kai ga taurin ran fuskantar Madina kai tsaye don yaqin Annabi SAW.
.
Wato aika-aikar da suka yi ba su jira sun ga sakamakon haka ba, sai ga 'yan leqen asirin muslunci sun dauko wa Annabi SAW labarin cewa Larabawan qauye fa na Banu Mahaarib, Sa'alaba da Gatfaan sun fara taruwa kuma Madina suka nufa, jin haka sai Annabi SAW ya riga su, ya dibi sojojinsa ya nufi Najad da su, don sanya tsoro a zukatansu, kuma kar su qara gangancin taba musulmai da muslunci, suna ganin isowar Annabi SAW da sahabbansa RA, sai duk suka watse, suka nufi duwarwatsu don samun mafaka.
.
Masana tarihi da yaqoqi sun bayyana cewa yaqin da Annabi SAW ya fita zuwa Najad ya faru ne a watan Rabee'ul Sani zuwa Jumadal Auwal shekara ta 4 Hijiriyya, wannan yaqin kusan dole ne ma musulmai su yi a daidai wannan lokacin, domin shekara na gabatowa, yaqi na gaba da aka sanya lokaci tare da Abu-Sufyan na kusantowa, in aka bari Larabawan da ke kan hanyar Makka zuwa Madina suka tafi a kan haka ba a tsorata su ba har Quraishawa suka zo, abin ba zai dadi ba, kuma an sara a gaba, girman da suke da ita kafin Uhud ta dawo, suka tabbatar da cewa in fa suka taba muslunci za su ji ba dadi.

Rubutawa:- Babban Manar Alqasim 
Gabatarwa:- Yusuf Ja'afar Kura

Daga 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)